Biyarafa: Abin kunya ne kalaman wasu shgabannin Arewa – Farfesa Ango
Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce shaida wa Aminiya cewa abin kunya ne kalaman da wadansu shugabannin Arewa ke furtawa a kan kisan da ’yan kabilar Ibo suka yi wa ’yan Arewa a kwanakin baya: Aminiya: Yaya kungiyarku take kallon sarakuna da gwamnonin Arewa kan kalaman da suke furtawa game da […]
Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce shaida wa Aminiya cewa abin kunya ne kalaman da wadansu shugabannin Arewa ke furtawa a kan kisan da ’yan kabilar Ibo suka yi wa ’yan Arewa a kwanakin baya:
Aminiya: Yaya kungiyarku take kallon sarakuna da gwamnonin Arewa kan kalaman da suke furtawa game da kisan gillan da ’ya’yan kungiyar neman kasar Biyafara ta IPOB ta yi wa ’yan Arewa?
Farfesa Ango: kungiyar da nake ciki ta dattawan Arewa mun riga mun yi jawabi a kan wannan batu, mun ce da farko dai wannan abu yadda aka fara shi ya nuna cewa mutanen Arewa musamman manyan Arewa da ake ganin cewa su manyan Arewa ne ba su san inda kansu yake yi musu ciwo ba. kila ma ba su san abubuwan da suke tafiya a kasar nan ba. Su dai suna nan sun kudundune a wuraren da ake ganin su manya ne, domin a lokacin da ’ya’yanmu da jikokinmu suka fito suka yi kokarin mayar da martani a kan irin iskanci da cin kashin da ’yan kabilar Ibo suke mana a kafafen watsa labarai na zagin iyayenmu da kakanninmu, kafin a ce haka a nan Arewa an fara jin yadda ake zaginsu, musamman gwamnoni su ne suka fito suka fara la’antarsu cewa bu su yi daidai ba. Akwai ma gwamnan da ya ce a kama su. A cikin sarakuna kuma akwai wanda ya ce shi ma zai zubar da jininsa wajen kare kabilar Ibo. Kwanan nan ko yau ne ko jiya ne, na samu labarin Mai alfarma Sarkin Musulmi ma ya ce da a kashe Ibo daya a garinsa ko a kofar gidansa gara jininsa ya zuba, ko a je a kashe shi. To amma ban sani ba ko yana kasar ne yake jin labarin cewa ana kashe jama’arsa, wato ana kashe mana jama’armu a can kasashen Ibo, ban yi tsammanin cewa za su bullo wa abin ta haka ba, tsammanina shi ne ya tabbatar da cewa yadda ake wulakanta mutanenmu a can, a sama ba za mu dauki matakin ramuwa ba yanzu, sai ya yi kokari ya tabbatar cewa ya tsaida, ku ya sa baki a tsaida barnar da ake wa mutanenmu a can tukuna. Sai an ba shi tabbacin cewa za a tsare jinin jama’armu da dukiyarsu a can, kuma ya tabbatar da haka sannan a matsayinsa na uba kuma shugaba sai ya kwatar mana da hankali cewa an tabbatar masa cewa halin tashin hankalin da jama’armu suke ciki a can zai canja, ba lallai sai an kai musu soja ba. Amma ai an gani saboda wannan barna da aka fara gwamnati ta ga dole ne a tsaida shi in ba haka ba kasar za ta rude, shi ya sa ta kai sojoji a can.
Saboda haka mene ne na kirarin cewa shi da a kashe Ibo a garinsa, ko a kofar gidansa, gara a zubar da jininsa, ko a kashe shi? Ni abin da na ji ke nan, kuma an ce an ji a kafafen watsa labarai da dama ya yi wannan maganar. To wannan magana a wurina abar kunya ce, kuma wannan furuci rage mutuncin mutanen Arewa ne gaba daya. Idan bai lura da rage nasa mutuncin ba, to mu ’yan Arewa muna ganin cewa ya rage mana namu mutuncin, a matsayinmu na mutanen Arewa wanda yake tinkaho cewa shi shugaba ne a ciki.
Baya ga furucin da aka ce sarakuna sun yi Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya ce ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ’yan ta’adda cewa bai dace ba, me za ka ce?
Wannan ka-ce-na ce da ake yi ko aka ce Sanata Saraki ya fada na bincika, kuma baki-da-baki, abinda ya tabbatar mana ya ce shi ne, kafin Shugaban kasa ya bar kasar nan ya tafi taron Majalisar dinkin duniya ya kamata ya sa hannu a wata doka wadda za ta tabbatar da cewa wannan kungiya haramtacciya ce, ya ce iyaka abin da ya fada ke nan, kuma alhamdulillahi an yi haka. Shi ya sa ma da yin haka aka kai wa kotu, ta tabbatar da wannan haramci, ina tsammani kafafen watsa labarai sun nuna kamar ya nuna abin da aka yi ba daidai ba ne, mun tambaye shi baki-da-baki ya yi bayani kuma mun gamsu.
Kun gamsu da matakin da gwamnati ta dauka na haramta kungiyar?
kwarai kuwa mun gamsu da haka, kuma idan gwamnati ba ta dauki wannan mataki ba ina amfaninta.
Wata matsala ita ce ta shigo da makamai, wane yunkuri kungiyarku ke yi na ganin an gano masu shigowa da su da daukar mataki a kansu?
Mun tattauna a kai, kuma za mu sa ido mu ga cewa an dauki duk matakin da ya kamata don gano musu shigowa da su da inda ake dauko su da matakan da za a dauka a kai. domin cinikayya da duk wata kasa ya halatta amma ba ta kazamar hanya ba. don haka za mu sa ido mu gani.
Ministan Watsa Labarai ya ce sun gano hedkwatar da IPOB ke da mazauni ko kun yi magana a kai?
Muna da masaniya a kai domin Ministan Watsa Labarai, ya ba da bayani a kan cewa kungiya ta Biyafara tana da ofishinta da akawunta wato inda take aje kudin da ake tara mata a kasar Faransa ne. Sai dai na ga gwamntin Faransa ko wakilinta a nan kasar ya fito ya yi musun wannan. Ya ce bai san suna nan ba, ko ba a san suna can ba. Ya ce kasarsu tana ba da dama mutane su bayyana ra’ayi, ko su yi abin da bai taka dokar kasa ba, ya ce yana gayyatar gwamnatin Najeriya ta je ta tattauna da shi a san gaskiya ko rashin gaskiyar wannan abu.
Ku akwai wani mataki da za ku dauka na ganin cewa an yi muku bayani a kai?
Eh ga shi muna ta yi muna tataunawa a kai kuma aikin da muke yi ke nan, kuma har yara sun fito su ma suna yi amma aka fito ana zaginsu, to sai ga shi yanzu gaskiya ta bayyana cewa a karkashin wannan abin da ake yi na iskanci a kasashen Ibo manyan shugabannin Ibo su suke goya musu baya. da sun ce a’a ba su san maganar ba amma ga shi gaskiya ta yi halinta an fito kuru-kuru su kungiyar Ohaneze da sun ce kada a kama Kanu ne fa, ga shi ya yi laifi, kuma ya saba duk wani alkawari da kotu ta ba shi kafin ta ba da belinsa amma an ce wai bai yi laifi ba. ’Yan uwansa sun ce kada a kama shi amma ga shi ana kashe namu ’yan uwan, kuma mun yi hakuri tare da sa ido tukunna mu ga me za a yi, kuma har yanzu ana so a rika dora mana laifi duk da hakurin da muke yi.