Biyu-babu a Masarautar Kano
A ranar Litinin din nan ne aka wayi gari da labarin sauke Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II daga karagar sarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi. Tun kafin a gudanar da zaben da ya mayar da Ganduje kujerar mulkin Kano a karo na biyu ne […]
A ranar Litinin din nan ne aka wayi gari da labarin sauke Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II daga karagar sarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi.
Tun kafin a gudanar da zaben da ya mayar da Ganduje kujerar mulkin Kano a karo na biyu ne aka fara sa-in-sa tsakanin Gwamnatin Kano da Mai martaba Sarki Sunusi II dangane da wani aikin samar da hanyar jirgin kasa da gwamnati ta so ta yi, wanda Sarkin yake ganin ba shi ne bukatar mutanen Kano ba.
Daga nan aka fara takun-saka tsakanin gwamnati da Masarautar Kano, har aka zo lokacin zaben Ganduje a karo na biyu inda aka yi zargin Mai martaba Sarki Sanusi bai mara wa Ganduje baya ba. Wannan ya sanya Gwamna Ganduje ya himmatu wajen ganin bayan Sarki Sunusi. A dalilin haka ne ya kirkiro sababbin masarautu guda hudu suka zama masarautu biyar har da ta Kano.
Tun a wancan lokaci ake ta rade-radin cewa Ganduje zai sauke Sarkin Kano daga sarautar Kano amma hakan bai yiwu ba saboda sanya baki da manya suka yi, hatta Shugaba Buhari ya kafa wani kwamiti da ya tura Kano domin a sasanta tsakanin Gwamna da Sarki, duk da haka sai kawai aka wayi gari ranar Litinin din nan da labarin tube Sarki Sunusi II.
Kowa ya riga ya fahimci inda Gwamna Ganduje ya fuskanta, wato tube Sarki Sunusi yake so ya yi, amma maimakon ya dumfari Sarkin shi kadai, sai kawai ya sanya sandar iko ya yi raga-raga da masarautar, inda ya kacaccala ta zuwa masarautu biyar, kuma ya ce duk sarakunan matsayinsu guda ne, wato kowanensu Sarki ne Mai daraja ta Daya kuma kowane zai iya zama Shugaban Majalisar Sarakuna, domin tsarin karba-karba za a bi, inda aka fara da Sarki Sunusi a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano, bayan wa’adinsa ya kare sai kuma wani Sarkin ya karba.
Wannan abu da Gwamna ya yi ya sanya ya rusa Masarautar Kano mai tsohon tarihi da kima da daraja, domin yanzu Masarautar Kano da a baya take da kananan hukumomi 44, ta koma tana da kananan hukumomi takwas ne kawai, wato ta tashi daga babbar masarauta a Najeriya zuwa ’yar karamar masarauta, duk dai an yi haka ne da nufin rage tasirin Sarki Sanusi. Hakan ya sanya an rage darajar Masarautar Kano da kuma ta Sarkin Kano, an yi biyu babu ke nan.
Kodayake shi Gwamna Ganduje cewa ya yi ya kara masarautu ne domin samar da ci gaba a yankunan Jihar Kano. Sai dai kuma abin da aka kasa fahimta shi ne, ta yaya a yau za a ce ta hanyar masarautu ne za a iya samar wa jama’a ayyukan ci gaba, alhali tuntuni an mayar da sarakuna hoto, sun zama matattarar al’ada da tarihi kawai?
Shi kansa marigayi Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayaro ya tabbatar da cewa sarakuna ba su da sauran iko, inda ya bayyana a wata hira da aka yi da shi da aka buga a wani littafi mai suna ‘Prince of the Times’ na Dokta Umar Farouk, cewa, ‘Da mu (sarakuna) muke yi, aka zo ana yi da mu, yanzu sai dai a yi a fada mana.’ To yanzu an kai lokacin da ko fada wa sarakunan ba a yi, sai dai kawai su ga ana yi. Ta yaya irin wadannan sarakunan za su samar da wani muhimmin ci gaba a yankunansu alhali su ma ta kansu suke yi? Marigayi Malam Aminu Kano ya taba cewa wani lokaci zai zo da talaka zai dubi Sarki yana zaune, ya ce ‘Sannu Sarki,’ ya wuce bai ko damu da shi ba.
Idan yawan masarautu na taimakawa wajen samar da ci gaban al’umma da yanzu yankin Kudancin Kaduna ya fi ko’ina a kasar nan ci gaba, saboda babu yankin da ya fi su yawan sarakuna, domin akwai kananan hukumomi masu manyan sarakuna guda uku-uku.
Yanzu dai za a iya cewa Sarki Sunusi ya cimma burinsa na zama Sarkin Kano, saboda a lokacin da yake Gwamnan Babban Banki an tambaye shi ko yana da ra’ayin zama Shugaban Kasa? Sai ya ce shi babban burinsa ya zama Sarkin Kano. Yanzu za a iya cewa shi ne Sarkin Babbar masarautar Kano mai kananan hukumomi 44 na karshe, kuma Sarkin Masarautar Kano mai kananan hukumomi takwas na farko, sannan Shugaban Majalisar sababbin masauratun Kano na farko.
Gwamnatin Kano kuma ta saro wa kanta aiki, domin dawainiyar da za ta rika yi da wadannan sarakuna biyar ba karama ba ce, saboda makudan kudi za ta rika kashewa wajen kula da su, kudin da ya kamata a iya amfani da su wajen inganta rayuwar al’umma baki daya, maimakon inganta rayuwar wadansu mutane ’yan kalilan.
Tsohon Sarki Sanusi ya nuna kamun kai da dattaku a ranar da aka cire shi, domin ya daure ya yi jawabi mai kashe jiki, inda ya bukaci jama’a su zauna lafiya kuma su bai wa sabon Sarki hadin kai da goyon baya. Ko lokacin da aka sauke shi a Gwamnan Babban Banki haka ya nuna karfin hali, domin yana wajen taro a kasar Nijar, labarin sauke shi ya same shi, nan take ya sauka daga kujerar da yake zaune ya umarci matar da take rakiyarsa ta maye gurbinsa.
Tsohon Sarki Sanusi mutum ne da ba ya iya ganin abu ya yi shiru, haka yake tun yana yaro, domin shi da kansa ya fadi cewa tun yana yaro bakinsa ke jawo masa matsala, inda ya bayar da labarin satar biskit da ake yawan yi wa dalibai a lokacin da suke makarantar rainon yara ta kwana ta Saint Ann da ke Kaduna, inda ya kalubalance matar da ke kula da su (metron) har ta mare shi, suka yi rikici saboda ta ce ya ce ta yi masa sata, amma daga nan ba a sake sace musu biskit din ba.