Bode George bai halarci taron yarjejniyar ’yan takarar shugabancin PDP ba
Mutum bakwai da suke neman mukamin shugabancin jam’iyyar PDP na kasa jiya sun sanya hannu a yarjejniyar zaman lafiya a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja. Wadanda suka sanya hannu a yarjejniyar sun hada da tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran da tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel da tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashid Ladoja […]

Mutum bakwai da suke neman mukamin shugabancin jam’iyyar PDP na kasa jiya sun sanya hannu a yarjejniyar zaman lafiya a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
Wadanda suka sanya hannu a yarjejniyar sun hada da tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran da tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel da tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashid Ladoja da tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar, Orince Uche Secondus da tsohon dan takarar gwamnan na jihar Legas, Jimi Agbaje da fitaccen mai harkar yada labarai, Cif Raymond Dokpesi da tsohon ministan wasanni da ayyuka na musamman, Farfesa Taoheed Adedoja.
Amma ana sa ran tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Bode George wanda bai halarci taron ya sanya hannu a yarjejniyar.