Bodejo ya musanta zargin halatta kudin haram a zaman kotu

Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya karyata zargin da a ke yi masaa  kan aikata laifuka 12 da ya hada da halatta kudin haramun.

Bodejo ya musanta zargin halatta kudin haram a zaman kotu

Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya karyata zargin da a ke yi masa  kan aikata laifuka 12 da ya hada da halatta kudin haramun da kuma hannu a tallafawa ayyukan ta’addanci.

Bodejo wanda ya gurfana a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis na maida bayani ne a kan zargin da a ka gabatar a kansa da Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ke yi, a karkashin mai sharia Inyang Ekwo.

A yayin fara shari’an a karo na farko, Hukumar ta bakin lauyanta Wahab Shittu, ta zargi Shugaban na Miyetti Allah da aikata laifin hallata kudin haram da ta ce, ya kai dalar Amurka milayan 2 da doriya. Bayan karyata tuhumar da ke yi masan, lauyan Hukumar EFCC ya bukaci kotun da ta sa ranar fara sauraron bayanai a kan karar da su ka shigar, sai kuam bukatar cigaba da tsare shi har zuwa lokacin.

Da ya ke mayar da martini, lauyan Shugaban na Miyetti Allah mai suna Ahmed Raji ya bukaci kotun da ta bada belin jagoran kamar yadda ya ce, ya gabatar tun a farko. Lauyan ya shaida wa kotun cewa, laifin da a ke tuhumar wanda ya ke karewan na cikin rukunin wadanda doka ta amince a ba da beli a kansu, bukatar da lauyan EFCC ya bayyana ja a kai.

A karshe kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda a ke tuhumar a hannun Hukumar ta EFCC, tare da sanar da ranar 20 ga watan nan ta Yuli a matsayin ranar yanke hukunci a kan bukatar ba da belinsa.