‘Boka Mai Kunkeli’: Yadda ’yan wasan kwaikwayo na dauri ke mutuwa
Daya daga cikin wasannin kwaikwayo na harshen Hausa da suka fi shahara shekaru kusan 30 da suka wuce shi ne “Idon Matambayi” na gidan talabijin na kasa, NTA, da ke Sakkwato. Daya daga cikin ’yan wasan da ke taka muhimmiyar rawa a wasan kuma shi ne Alhaji Muhammadu Khadi, wanda ke fitowa a matsayin Boka […]
Daya daga cikin wasannin kwaikwayo na harshen Hausa da suka fi shahara shekaru kusan 30 da suka wuce shi ne “Idon Matambayi” na gidan talabijin na kasa, NTA, da ke Sakkwato.
Daya daga cikin ’yan wasan da ke taka muhimmiyar rawa a wasan kuma shi ne Alhaji Muhammadu Khadi, wanda ke fitowa a matsayin Boka Mai Kunkeli.
Kasancewar shi boka a wasan, matsaloli da dama—na lafiya, ko na zamantakewa, ko ma na tattalin arziki—shi ake tunkara da su.
Lokaci ya yi
Ranar Litinin ne dai aka ba da sanarwar rasuwar Alhaji Muhammadu Khadi, wanda ya bar duniya bayan gajeruwar rashin lafiya ta kwana uku a wani asibiti mai zaman kasa a birnin Sakkwato.
Ya rasu yana da shekara 78 a duniya, sanadiyar hawan jini da ciwon suga da ya daɗe yana fama da su.
Marigayin ya bar matan aure hudu da ’ya’ya 30 da jikoki 54 da kama-kunne hudu, dukkansu suna cikin alhinin rashinsa.
Mutuwar tasa na zuwa ne kusan shekara biyar bayan rasuwar Alhaji Muhammadu Danmalam (wanda ya rasu a watan Nuwamban 2015), wanda ke fitowa tare da marigayin a matsayin Dan Wanzam.
‘Bango ne shi…’
Aminiya ta zanta da kanen margayin na uku, Garba Khadi, wanda a madadin iyalansa gaba daya ya ce sun yi rashin bango a gidansu saboda yadda yake taimaka musu da shawarwari da sanya su kan haryar ci gaba da hade kan ’yan uwa wuri daya don kara dankon zumunci.
“Margayi ya yi rayuwa mai kyau ba ya da fada in ka zauna da shi zai ba ka dariya, ba ya wasa da hakkin makwabta.
“Muna da dangantaka mai kyau da shi; ga son addini da Sallah”, inji Malam Garba.
Rayuwarsa da yarinta
Ya ci gaba da cewa marigayin ya yi karatunsa na firamare ne a Makarantar Magajin Gari, daga nan ya je Makarantar Sakandare ta Sarkin Musulmi Abubakar.
Bayan ya kammala ya yi aikin malanta da LEA a Sakkwato, daga baya ya sauya aiki ya koma kotu a matsayin muhutin alkali, inda ya shekara biyar.
Daga nan ya koma wani bangaren ya karanci harkar lafiya a Makarantar Horar da Jami’an Kiwon Lafiya ta Sakkwato inda ya karanci kiwon lafiyar al’umma kafin ya yi ritaya ya zauna Asibitin ’Yar Akija.
Bayan nan gwamnatin jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Aliyu Wamakko ta nada shi mamba a kotun Sasanta Rikice-rikicen Gidan Haya, wato Rent Tribunal—aikin da yake kansa ke nan.
Ribar Wasan Kwaikwayo
Marigayin ya ci ribar wasan kwaikwayo soasai, inji Alhaji Garba, domin kuwa, shahararsa a wasan ta yi masa sanadin zuwa aikin Hajji har sau 20, bayan alfarma da kyaututtukan da ya samu.
Bashar Abdullahi A. Jo, daya daga cikin yaran Boka a wasan kwaikwayo, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa a shekara 26 zuwa 27 da ya yi da marigayin ya san shi mutum ne mai amana da son jama’a.
“Yana son ya ga mun taso domin mu maye gurbinsu a wasan Hausa domin ba shi son harkar ta mutu a kishinsa da harshen Hausa”.
Ya kuma ce marigayin ya ba su tarbiyar bin na gaba da tsayawa tsayin kan daka a wurin aiki don bayar da abin da ake bukata.
“Na yi rashin maigidana sila ta ta shiga wannan harkar; na koyi hakuri da son jama’a da gaskiya da alkawali a wurinsa.
“Sai bayan an rufe shi ne na kara tabbatar da rashin da na yi”, in ji shi.
Shugaban kungiyar ‘yan wasa a Sakkwato Abdul Isma’il Musa ya ce a lokacin da ya ji rasuwar ya kadu sosai domin marigayin yana cikin jagororinsu a wannan harka.
“A lokacin da aka zabe ni na jagoranci ’yan wasa sai da muka karrama margayin saboda rawar da ya taka ga ci gaban harkar. Lokaci-lokaci muna nemansa shawara kan abin da za mu yi”.
Kalaman ’Yar Mai Albasa
Ya kuma ce sun koyi darussa a zaman da suka yi da shi duk da ba su yi wasa tare ba domin shi mutum ne mai son ci gaban matasa.
Daya daga cikin manyan taurarin “Idon Matambayi” da suka rage, Malama Mai Kwasa Isa, wadda aka fi sani da ’Yar Mai Albasa, ita ma tana fama da rashin lafiya a gidanta lokacin da wakilinmu ya ziyarce ta domin samun wasu bayanai game da rayuwar margayin.
“Yanzun da ka gan ni daga asibiti nake komai ban iya cewa ina jin jikina, ga mu dai ban san tazararar da ke tsakaninmu ba a barin duniyar nan”, in ji ‘Yar Mai Albasa.