Boka mai taimakon ’yan fashi ya shiga hannu a Shagamu
Jami’an ’yan sanda na musamman masu yaki da ’yan fashi da makami a Jihar Ogun sun yi nasarar kame wani boka da ake zargi da yin kaurin suna wajan tallafa wa ’yan fashi da siddabaru; inda ’yan fashin kan nemi sa’a a wajensa don yin miyagun ayyukansu.A cewar mai magana da yawun ’yan sandan Jihar […]
Jami’an ’yan sanda na musamman masu yaki da ’yan fashi da makami a Jihar Ogun sun yi nasarar kame wani boka da ake zargi da yin kaurin suna wajan tallafa wa ’yan fashi da siddabaru; inda ’yan fashin kan nemi sa’a a wajensa don yin miyagun ayyukansu.
A cewar mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Ogun, DSP Olumuyiwa Adejobi, jami’an sun yi nasarar kame hatsabibin bokan ne mai suna Musiliyu Otun Afeez a garin Shagamu a karshen makon jiya, bayan binciken da rundunar ta dade tana yi a kansa. An kuma same shi da bindigogi da albarusai da kayyayakin tsafe-tsafe kamar layu da guru da sauransu.
Har ila yau, rundunar ta yi nasarar kame Kabiru Soyemi a garin na Shagamu, wanda ake zargi da kasancewa dan kungiyar asiri da fashi da makami, inda aka same shi da bindigar gargajiya, yayin da sauran gaggan ’yan kungiyar tasu suka arce. Mutane biyun da ake zargi, suna ba ’yan sandan hadin kai wajan bayar da bayanai.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Abdulmajid Ali ya yaba da kokarin rundunar tasa, ya kuma lashi takobin kara jajircewa don hana duk wani batagri sakat a jihar.