Boka ya harbe mai neman maganin bindiga har lahira

Boka ya bindige marigayin ne a lokacin da yake kokarin gwada maganin bindigar da ya hada masa.

Boka ya harbe mai neman maganin bindiga har lahira

Wurin Tsafi

’Yan sanda a Jihar Enugu sun damke wani boka da ake zargi ya harbe wani da ya nemi maganin bindiga a wurinsa a yankin Karamar Hukumar Isi-Uzo.

Aminiya ta samu rahoton cewa, bokan ya harbe mutumin har lahira a lokacin da yake kokarin jarraba ingancin maganin bindigar da ya hada masa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya bayyana a ranar Talata cewa, bokan ne ya kera bindigar da ya yi amfani da ita wajen harbe mutumin.

Binciken farko da ’yan sandan suka gudanar ya nuna bokan ya amsa cewa lallai ya yi amfani da bindiga kirar gida wajen harbin da ya yi sanadiyar mutuwar mutumin a inda yake sana’arsa ta tsubbace-tsubbace.

Bokan ya ce hakan ya faru ne lokacin da yake kokarin gwada maganin bindigar da ya hada wa marigayin.

Ndukwe ya ce batun na hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar inda ake ci gaba da bincike.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan