Boka ya sa budurwa ta jefa jaririn da ta haifar masa a masai

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Jihar Jigawa, Alhaji Muhammed Gidado ya ce sun kama wata budurwa mai suna Hadiza Shehu wadda ta haifi jariri ta jefa a masai a tsakiyar daren ranar Asabar da ta gabata.  Shugaban wanda ya shaida wa manema labarai haka a Dutse, ya ce budurwar ta jefa jaririn […]

Boka ya sa budurwa ta jefa jaririn da ta haifar masa a masai
Boka ya sa budurwa ta jefa jaririn da ta haifar masa a masai

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Jihar Jigawa, Alhaji Muhammed Gidado ya ce sun kama wata budurwa mai suna Hadiza Shehu wadda ta haifi jariri ta jefa a masai a tsakiyar daren ranar Asabar da ta gabata.  Shugaban wanda ya shaida wa manema labarai haka a Dutse, ya ce budurwar ta jefa jaririn a masai ne sakamakon umarni da bokanta ya ba ta na cewa da ta haifi yaron ta kashe shi in ba haka ba asirinta zai tonu kuma za ta iya gamuwa da aljanu.
Ya ce Hadiza ta ce bokan da ake kira Malami Malam Akarami mai kimanin shekara 42 shi ne ya yi mata ciki a lokacin da ta je wurinsa neman taimako samun aboki ko saurayi, sai bokan ya yi amfani da wannan dama ya kai ta dakinsa ya yi lalata da ita daga nan ne ta samu cikin da ta jefa dan a masai.
Shugaban ya ce Akarami ya dade wajen harkar damfara (419), kuma shi ya ba ta umarnin ta jefa yaron cikin masai in ba haka ba za ta gamu da aljanu wadanda za su iya yi mata illa, kuma kada ta yi kokarin tona masa asiri in kuma ta ki za ta gane kurenta.
Ya ce bokan ya ce mata muddin ta ki bin umarnin da ya ba ta zai gama ta da aljanu lamarin da ya sa ta jefa jaririn a cikin masai da nufin kauce wa aljanun Akarami, amma sai jami’an tsaro suka yi nasarar kama ta da bokanta don su fuskanci hukuncin da ya dace da su.
Ya ce wadanda ake tuhumar nan ba da bata lokaci ba za a gabatar da su a gaban kotu domin yi musu hukuncin da ya dace.