Boka ya sa matasa sun yi fawan abokinsu

Al’ummar Unguwar Zubairu da ke Mangwaro-Biyu a karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna sun wayi gari cikin firgici da ximauta bayan da suka iske gawar wani xansu mai suna Zubairu Abubakar mai shekara 22, an yi masa yankan rago tare da yin fawan gawarsa.Aminiya ta ziyarci kauyen domin tantance yadda lamarin ya wakana, inda mahaifin […]

Boka ya sa matasa sun yi fawan abokinsu
Boka ya sa matasa sun yi fawan abokinsu

Al’ummar Unguwar Zubairu da ke Mangwaro-Biyu a karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna sun wayi gari cikin firgici da ximauta bayan da suka iske gawar wani xansu mai suna Zubairu Abubakar mai shekara 22, an yi masa yankan rago tare da yin fawan gawarsa.
Aminiya ta ziyarci kauyen domin tantance yadda lamarin ya wakana, inda mahaifin marigayin, Liman Abubakar Zubairu wanda ke jinyar karaya sanadiyyar rusawar gini a kansa ya shaida mata cewa, “A ranar Talata bayan Magariba muna tare da marigayin sai aka kira shi ta bayan gida sai ya nemi yardata har ya karbi aron tocilata ya fita. To daga nan bai dawo ba har karfe 12:00 na dare, sai hankalinmu ya tashi ganin bai taba kai haka ba, kuma kusan shi yake kula da ni, saboda shi ne babban xana, saboda sai da na shekara 55, don haka muka kwana ba mu iya barci ba saboda tunanin halin da yake ciki.”
Mahaifin ya ce da gari ya waye xan wansa zai shi gona da misalin karfe 7:00 na safiyar Larabar makon jiya, sai kawai ya ga gawar Baba cikin wani hali ya rugo a guje ya faxa wa ’yan uwa aka xunguma zuwa wurin aka xauko gawar. “Jin yadda aka yi masa sai na ce a wuce da shi can gidan wana,” inji shi.
Mahaifiyar marigayin Malama Raliya cikin kuka ta bayyana wa wakilinmu cewa, “marigayin ne ma ya yanka mata kubewar da na yi miya da ita a ranar. Ya ce mama ina jin yunwa in kin gama tuwon ki sa min da yawa sannan ya tambaye ni in ba shi Naira goma, sai na kawo Naira ashirin na ba shi rabuwana da shi ke nan sai na ji wannan mugun labari a kansa,” inji ta.
Mai unguwar garin Malam Umaru Musa wanda da shi ne aka xauko gawar marigayin aka yi masa wanka ya ce “Yadda na ga gawar ba ta da kyan gani domin yankar rago suka yi masa kuma suka cire makogoronsa da harshensa da kuma agaran kafafunsa, suka kuma zare jijiyoyin hannayensa biyu, tare da yanke farjinsa. Wannan ne halin da muka samu marigayi Zubairu, bayan na jawo hankalin al’ummar unguwana da su kwantar da hankulansu, sai kuma na sanar da hakimina tare da jami’an ’yan sanda, nan take suka zo suka duba bayan sun yi abin da duk ya kamata su yi sai suka ba da umarni a yi masa sutura.
Daga nan sai muka xauki matakin kula da yanayin zirga-zirgar jama’armu cikin ikon Allah da dare sai muka gano xaya daga cikin yaran unguwa kuma makkwabcin gidansu, mai suna Abubakar Iliyasu da wani irin kamanni da ba mu gane ba, nan fa muka fara bincikensa, muka ga wasu abubuwa na ban mamaki a wajensa kuma kayan da suke jikinsa a lokacin da suka yi wannan aika-aika duk sun baci da jinni, ya bayyana cewa wani boka ne ya sanya  su su kawo masa sassan jikin mutum zai bas u Naira 150, kuma ya faxa mana cewa xaya daga cikin abokan aikinsa mai suna Yusuf Ibrahim wanda aka fi sani da Battu Bafulatani, rugarsu na nan a kusa da mu, shi ma mun je  mun samu kayayyakin da suka kashe marigayi da su, kamar wukake da sauransu, tuni muka  mika su ga ’yan sanda.”
Binciken da Aminiya ta yi ta gano cewa bokan da ya sa matasan suka kashe abokinsu ya gudu daga garin bayan da ya ji an kama yaran.
Mataimakin Kwamishinan ’Yan sandan Mai kula da Shiyya ta Xaya da ke Zariya, Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a wannan xanyen aiki kuma sun baza komarsu domin kamo wanda ake zargin ya sa su.