Boka ya shiga hannu kan sace tifa

An kama bokan ne bayan ya haɗa baki da direban wata tifa suka yi awon gaba da ita

Boka ya shiga hannu kan sace tifa

An kama wani boka kan sace wata motar ɗaukar kaya mallakin wani kamfani a Jihar Bibuwai.

Noman ya shiga hannu ne tare da wani direba a kamfanin gine-gine na CHEC da ke aikin gyaran tituna a jihar.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Bibuwai, Catherine Aneneh ta ce a ranar Asabar suka samu rahoton cewa direban ya yi awon gaba da morar da aka tura shi ya kai duwatsu daga Ƙaramar Hukumar Ohimini LGA zuwa yankin Mase da ke Ƙaramar Hukumar ta Gabas inda ake aikin gyaran titi.

Ta ce daga bisani aka direban da bokan bayan an sami motar hannunsu a yankin Ikyurav da ke Ƙaramar Hukumar Kwande.

Catherine Aneneh ta bayyana cewa direban ya kasa bayar da cikakken bayani kan dalilinsa na kai motar wurin bokan, kuma ya kashe wayarsa tsawon kwana huɗu da ake nemansa.

Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —Babangida

Yadda aka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga

Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan mangwaro a makaranta

NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri