Bokan da ke hada wa ’yan ta’adda maganin bindiga ya shiga hannu

A cewar ‘yan sanda, bokan na shirya maganin ne kan farashi N60,000 don amfanin ’yan fashin daji da makamantansu.

Bokan da ke hada wa ’yan ta’adda maganin bindiga ya shiga hannu

‘Yan sanda

Wani boka da ke shirya wa ’yan ta’adda maganin bindiga a Jihar Katsina, ya fada a komar ’yan sanda.

Baya ga shirya hada bindigar, bokan kan yi wa ’yan ta’addan addu’ar kariya don kada a kama su.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya shida wa manema labarai ranar Talata a Katsina cewa bokan da aka cafke na zaune ne a yankin Karamar Hukumar Sabuwa ta jihar.

Ya kara da cewa, sun samu nasarar damke shi ne sakamakon bayanan sirri da suka samu a kansa.

A cewarsa, bokan na shirya maganin ne kan N60,000 don amfanin ’yan fashin daji da sauran gaggan masu laifi a jihohin Katsina da Kaduna da kuma Zamfara.

Isah ya ce bokan ya amsa laifin da ake tuhumar sa, tare da cewa za su gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.

(NAN)