Bokan da ya boye matar aure shekara hudu zai shekara daya a kurkuku

Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse Mai shari’a Ibrahim Yusuf Harbor ya daure wani boka mai suna Umar Sa’id Yarma shekara uku a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira dubu 90, bayan da ya same shi da laifin boye matar aure na tsawon shekara hudu tare da kulla aure da ita har […]

Bokan da ya boye matar aure shekara hudu zai shekara daya a kurkuku

Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse Mai shari’a Ibrahim Yusuf Harbor ya daure wani boka mai suna Umar Sa’id Yarma shekara uku a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira dubu 90, bayan da ya same shi da laifin boye matar aure na tsawon shekara hudu tare da kulla aure da ita har suka haifi ’ya’ya biyu.

’Yan sanda ne suka gufanar da boka Umar Sa’id Yarma mai kimanin shekara 35 a gaban kotun, inda ya shaida wa kotun cewa ya yi wa matar mai suna Hafsa Sa’idu sihiri ne wajen juyar mata da tunani inda ya binne sihirin a kofar dakinsa don hana ta fita daga gidan. 

Bayanan da Aminiya ta samu sun ce iyayen Hafsa da suke zaune a karamar Hukumar Gwaram sun yi ta neman Hafsa a tsawon shekara hudu ba su ganta ba, sai daga baya ne suka samu labarin cewa an gan ta a kauyen Yarma da ke karamar Hukumar Birnin Kudu a wajen bokan. 

Sai dai bokan ya ce iyayen Hafsa ne suka mallaka masa ita a kauyensu da ake kira Langwami da ke karamar Hukumar Dutse. Amma Hafsa ta musanta sanin kauyen Langwami, kuma ta musanta bayanin da ya yi cewa mahaifanta sun rasu inda ta ce suna nan da ransu 

Majiyarmu ta ce kafin aukuwar hakan, iyayenta sun taba kai ta neman magani a wurin bokan da ta koma ne domin amsar magani sai bokan ya yi mata sihiri ya boye ta.

Majiyarmu ta ce bayan iyayen sun gano inda ’yarsu take ne sai suka sanar da ’yan sanda wadanda suka kama shi suka gabatar da shi a gaban kotu.

Da yake amsa tambayoyin alkalin boka Umar ya ce duk laifuffukan da ake tuhumarsa ya aikata, ya ce ya yi amfani da sihiri ne wajen sauya mata tunani kuma ya yi amfani da wata laya ce domin hana ta ficewa daga gidansa, kuma ya tono sihirin da ya yi mata ya bai wa ’yan sanda a lokacin da suke bincike a kansa. 

Bayan sauraren bayanin bokan ne Mai shari’a Ibrahim Yusuf Harbor, ya yanke masa hukunci kan laifuffuka uku da ake tuhumarsa a kai da suka hada da yin aure a kan aure da laifin boye matar aure da kuma laifin juyar da kwakwalwar matar wani domin ya mallake ta, inda aka yanke masa hukuncin zaman shekara daidaya a kan kowane laifi ko kuma tarar Naira dubu talatin-talatin.

Alkalin ya ce laifuffukan da bokan ya aikata sun saba wa sassa na 232 da na 92 da kuma na 407 na kundin manyan laifuffuka na Jihar Jigawa.

Kuma kotun ta ce babu aure a tsakanin bokan da Hafsa har abada, kuma kotun ta umarci Hafsa ta je ta yi istibra’i idan suna son juna da mijinta na baya su daidaita ta koma wajensa. 

Mijin matar mai suna Malam danladi Sara da ke karamar Hukumar Gwaram ya fada wa kotun cewa idan matarsa Hafsa da ya rasa tsawon shekara hudu ta kammala istibra’i zai mayar da ita su ci gaba da zaman aure.