Bokayen Indiya na kwasar kudi a Abuja

A yanzu dai kakar bokayen Indiya a Abuja ta yanke saka inda suke kwasar kudi ta hanyar da a cewarsu taimakon mutane suke yi.  Wadannan bokaye sun sanya allunan tallace-tallacensu a jikin bishiyoyi da turakun wutar lantarki a hanyoyin Abuja. Sun rubuta ‘Indian Temple’ da lambar wayoyi da irin ayyukan da suke yi a jikin […]

Bokayen Indiya na kwasar kudi a Abuja

A yanzu dai kakar bokayen Indiya a Abuja ta yanke saka inda suke kwasar kudi ta hanyar da a cewarsu taimakon mutane suke yi.  
Wadannan bokaye sun sanya allunan tallace-tallacensu a jikin bishiyoyi da turakun wutar lantarki a hanyoyin Abuja. Sun rubuta ‘Indian Temple’ da lambar wayoyi da irin ayyukan da suke yi a jikin allunan tallace-tallacensu, inda suke bayyana za su sanya mutum ya zama hamshakin mai kudi cikin kankanen lokaci, kuma za su magance matsalar rayuwar aure walau ta rashin haihuwa ko yadda za a mallake miji ko ta ofis ko ta kasuwanci da sauransu. Wakiliyar Aminiya da ta ziyarci irin wadannan bokaye ta ruwaitu abubuwan da ta fuskanta kamar haka:
Mutane da yawa ciki har da ni ba mu dauki tallace-tallacen wadannan bokayen da muhimmanci ba, wani lokaci nakan ce “wane shashasha ne zai yarda da wadannan soki-burutsun. Domin babu abin da ya fi, face mutum ya jira Allah Ya amshi addu’arsa.” Daga baya tunanina ya canja, na kuma tabbata duk yadda na dauki al’amarin to fa ya wuce nan.
A kan hanyata ta zuwa wani aiki a makon jiya sakamakon yadda ake kara samun yawaitar allunan tallace-tallace a jikin bishiyoyin da ke Abuja, na ci karo da tallace-tallacen ‘Indian Temple’, don na samu tabbaci sai na kira lambobin da aka sanya a jikin allunan, kuma na nuna musu ina bukatar aikinsu. Na yi haka ne don na ji dalilin da ya sa suke sanya allunan tallarsu a jikin bishiyoyi maimakon kan allunan talla da aka tanadar. Bayan na kira wata lamba da ke jikin allon talla na ‘Indian Temple’, sai al’amarin ya ba ni mamaki hade da girgiza ni.
Kamar yadda na yi wa sauran wadanda na kira na shaida musu ina neman taimako ne, na yi haka ne don kada idan sun fahimci ni ’yar jarida ce su ki saurarena.
Sai da na kira kamar mutum uku kafin na samu wanda ya iya magana da Turanci sosai, na ce masa ni bakuwa ce, ina kawo wa ’yan uwana ziyara a Kubwa, sai na ga tallace-tallacensu, kuma na yi sha’awar hulda da su, sai suka ce na same su gobe, sannan suka ce za su ba ni adireshi da kuma lambar sirri da idan masu gadi suka tambaye ni zan fada musu.
Washegari bayan na isa adireshin da suka ba ni, sai abin ya ba ni mamaki domin ban ga wata alama ta nuna ‘Indian Temple’ ba. Don haka sai na kira don na tabbatar da adireshin da aka ba ni babu kuskure. A nan suka ce na duba zan ga wani allo an rubuta ‘Help the Future Foundation……realizing your dreams.’ Idan na gani sai na shigo nan ne wurin. Bayan na ga allon ne, sai abin ya daure mini kai, na kuma tambayi kaina me ya sa suka yi basaja ta hanyar rubuta cibiya maimakon ‘Indian Temple’ da suke rubutawa?
Daga nan na nufi bakin kofar ginin, nan-da-nan kamar an jeho shi, wani matashi da ke zaune cikin wata lema ya nufo ni. Bayan ya iske ni sai ya tambaye ni me ke tafe da ni, ko kuma na yi batan kai ne? Cikin mamaki na tambaye shi me sa ya yi mini wannan tambayar, ko ya ga na yi kama da wacce kanta ya juye ko kuma ba ta san hanya ba? Idan har ban san wurin da na nufa ba, ai ba zan tunkari kofar wannan ginin ba. Sai ya ce: “Ba kowa ne yake shiga nan ba har sai an yi masa izini ko kuma ya zo da wata shaida da ke ba da izinin shiga.” Ana cikin haka ne wani matashi kuma ya sake fitowa, shi ma ya tambaye ni matsalata.  Na fada masa yadda aka yi na san wurinsu. Bayan na yi masa bayanin komai ne, sai ya ce na fada masa lambar sirrin da aka ba ni, sai na fada masa, bayan ya rubuta ne sai ya shiga ciki, da ya fito ne na ga ya saki fuskarsa, sannan ya ce mu shiga ciki. A lokacin da muke shiga, sai ya tambaye ni daga Kubwa ko, sai na ce masa eh.
Daga nan ya ba ni hakuri, kuma ya sanar da ni ’yan jarida sun sha yunkurin buga labari a kansu, hakan ne ya sanya suke daukar dukkan matakan da suka dace. “Dole mu dauki matakan kare kwastominmu daga mutane musamman ma ’yan jarida. Ba ma bukatar ’yan jarida, da su ko babu muna taimako hade da canja rayuwar mutane. Za ki iya tambayar kwastomominmu na hakika idan kina shakka. Ki tambaye su ko sun taba yin nadamar yin hulda da mu,” inji shi.
Harabar ginin cike yake da manyan motoci na alfarma. Hakan ya sa na ce cikin zuciyata: “Idan har mutane sun mallaki dukiya irin wannan, me zai sa su zo nan? Lallai kwadayin dan Adam ba ya da iyaka. Ganin yadda nake kallon motocin ne, sai ya ce mini ai da ma na fada miki ba ma saba wa mutane. Na yi murmushi a lokaci guda na gyada kai.
Akwai mutane da yawa a wurin wadanda suka hada da samari da ’yan mata, matasa da tsofaffi, dukansu suna jiran a biya musu bukatarsu. Aka ba ni wurin zama, a wurin akwai akalla mutum 20. A kusa da ni wata budurwa ce ta yi mini murmushi, sannan ta gaishe ni. Daga nan ta miko mini wata takarda mai dauke da sunayen yaruka, sannan ta bukaci na zabi yaren da nake so na yi magana da shi. Abin ya ba ni mamaki, na kuma tambaye ta me hakan yake nufi, sai ta sanar da ni ba kowa ne ya iya magana da Turanci ba, don haka suka tanadar da wadanda za su taimaka wurin yin cikakken bayani ga “Guru” (wato bokan Indiya). A nan na zabi Turanci.
Zabar Turanci da na yi ya sanya na zama ta uku, kasancewar sauran sai an jira wadanda za su yi musu tafinta. Daga nan na natsu don jin hirarrakin da ake yi a wurin.
A wata kusurwa ne na ji wata budurwa da wanda zai yi mata tafinta suna tattaunawa. Ta ce masa daga Benin take, ta dade tana fafutika amma kamar an shuka dusa. “Don haka a shirye nake na yi dukkan abin da Guru ya umarce ni, domin bayan kawata ta ziyarce shi ne ba da jimawa ba ta yi sallama da talauci. Hakan ya sanya na rika damunta don ta fada mini sirrinta, na sha wahala kafin ta yi mini bayani,” inji ta.
Bayan nan ne kuma sai wata mata ta shigo da ganinta ta jima tana harkar, bayan ta gaishe da su Guru ne ta ba su hakuri zuwan da ta yi. Ba tare da sirrintawa ba ta ci gaba da magana: “Ba ni da masaniyar ko ubangidana zai amince na yi tafiya gobe. Hakan ya sanya na garzayo don na karbi lakani don kada ya hana ni kudin tafiyar da na tambaye shi.
“Bayan haka ina so na shirya sosai yadda zan gana da wadansu mutane a Landan don kada su hana ni abin da zan bukata a wurinsu,” A nan Guru ya ce mata kada ta damu, “bayan kin kira mu ne na dukufa wurin hada miki lakanin kuma an samu nasara na kammala. Ba sai na tsaya yi miki bayani ba, domin kin san yadda ake amfani da shi. Kamar na kullum ne. Idan kin kiyaye sharuddan dole su ba ki kudin da kika bukata,” inji Guru. Bayan ta karba ta yi masa godiya hade da alkawarin idan ta dawo za ta ba shi ladan aiki.
Da layi ya zo kaina sai na shiga cikin dakin da Guru yake, na gan shi sanye da wata babbar riga mai hadakar ruwan gwal da fari da kuma ja, ya yi rawani da bakin yadi, bayan ya jijjiga kansa sai ya ce: “Madam kin sha wahala a rayuwa, amma ki kwantar da hankalinki komai zai zo karshe.”
A jikin bangwayen dakin akwai madubai. Bayan wani lokaci sai ya ce na duba daya daga cikin maduban da nake so, kafin na yi hakan sai na karanta Ayatul Kursiyyu. Bayan na kalli madubi daya sai ya ce na mike hannuwana, don ya yi mini duba. Bayan wani lokaci sai ya ce akwai abubuwan alheri da aka kaddara su a kaina, amma makiyana sun yi mini katanga, don haka daga yau duk inda kika je har kika yi magana ta zauna ke nan,” inji shi.
Daga nan ya dauko wata roba, sannan ya umarce ni na dauki daya daga cikin abubuwan da ke ciki, sai na ce masa ina azumi, sannan na roke shi mu sanya lokaci bayan azumi, na ci sa’a ya amince.
A nan ya ba ni jerin abubuwan da zan kawo ciki har da gashin kai da zan yanka da misalin karfe 2:00 na dare, na kuma zo da farin yadi da fari da bakin attaruhu da farin goro shida da farin kyandir da talo-talo biyu. Idan kuma ban san inda zan samu ba, to sukan sayar da kowane daya Naira dubu 20; biyu dubu 40 ke nan.
Bayan na karbi jerin abubuwan da zan so da su ne na yi alkawarin dawowa mako mai zuwa. Bayan na fito ne na sake ganin wurin ya dinke da mutane. A zuciyata dai ina ta addu’a Allah Ya kiyaye ni.
Daga nan na sake kiran wani Gurun, bayan na yi bincike sosai ne na gane a Jihar Nasarawa yake, amma yana da yara a Abuja, a nan na yi masa bayanin yadda nake fama da talauci da kuma burina na son zama mai kudi.
“Kada wannan ya daga miki hankali, idan kin zo wurina kika kalli madubi, matsalarki ta kare, idan ma wani ne ya sa miki hannu za ki gane. Idan kudi kike nema za ki zo da jariri.”
 “Jariri kuma?” Na tambaya a tsorace. “Haka na ce, jaririn zai samar miki da Naira miliyan 375. Idan kina son fin haka kuma sai ki zo da jarirai,” inji shi.  
Daga nan sai ya ce “idan kuma ba ki da hanyar da za ki samu jariri, akwai likitan da zai kawo, amma za a ba shi Naira dubu 230, kuma likitan ne zai ba ki jaririn ke kuma ki kawo mini. Na yi wa mutane da yawa aiki ciki har da ’yan siyasa. Bayan mun yi miki aiki kin samu kudin kada ki ajiye a banki, ki zuba hannun jari, misali ki sayi gidaje ko ki gina su. Kuma idan za ki zo, ki taho da wani da kika yarda da shi, wanda ba zai tono asiri ba.”
Daga nan ya ba ni jerin abubuwan da zan kawo idan zan zo wurinsa. Ya ce “Babu bukatar ki zo da kudi, saboda za ki bar wurinmu da kudi, daga kin zo, kuma kin zama tamu, don haka babu bukatar ki biya mu domin tarayyarki da mu ita ce biyanmu da za ki yi.”