Boko A kasar Hausa (6)

A tuna ba tun yau ba Musulmi ke kallon tsarin mulki a matsayin kishiya ga addinin Musulunci, shi ya sa ma wasu ke ce da tsarin constitution da ake gabatarwa , mai ‘kwance tushe,’ wato mai raba Musulmi da addininsa. Shi ya sa ko da ake rantsar da shugabannin kasar nan, suna rataye da kur’ani, […]

Boko A kasar Hausa (6)

A tuna ba tun yau ba Musulmi ke kallon tsarin mulki a matsayin kishiya ga addinin Musulunci, shi ya sa ma wasu ke ce da tsarin constitution da ake gabatarwa , mai ‘kwance tushe,’ wato mai raba Musulmi da addininsa. Shi ya sa ko da ake rantsar da shugabannin kasar nan, suna rataye da kur’ani, suna cewa za su tabbatar da sun kare constitution, wasu ke ganin an yi kaza da kan zabo ne. Dimokuradiyya ga ‘yan wannan kungiyar kuwa ba ta komai sai tabbatar da zalunci da cin hanci da almundahana! Shi ma wannan ba sabon abu ba ne, mun dade tare da shi! Batun da kungiyar ke yi na cewa ilmin boko na lalata tunani da tarbiyya, shi ma ba bako ba ne a rayuwarmu ta yau da kullum, kamar yadda muka gani tun a farkon wannan tambihi. Saboda haka idan aka natsu za a ga cewa akwai alaka ko dai ta tunani ko manufa tsakanin Boko Haram da Boko Akidah da Boko Sana’a da kuma Boko Halal! Yadda za a rarrabe tsaki daga cikin tsakuwa shi na abin yi.

A lokacin da muka zo kan wannan gaba ya dace a fahimci wani abu. Duk inda ka shiga a duniyar nan tamu, kuma duk inda ake gwabzawa tsakanin masu ra’ayin neman kawo sauyi ko dawo da martabar addinin Musulunci ta kowace irin fuska za a samu cewa kungiyoyi biyu ne ke tashe, ko dai ‘yan ta’adda ko kuma ‘yan kwatar ‘yanci, sai wanda ka zaba ko ka amince da shi. Misali, ‘yan Taliban a Afghanistan, ‘yan tada-zaune-tsaye ne ga Amurka da Yammacin Turai, amma ga wasu mutanen kasar Afghanistan da wasu Musulmi fa, ‘yan kwatar ‘yanci ne! kasar Iran da Palasdinu, masu tada- zaune-tsaye ne ga Amurka da wasu kasashe na Yamma, amma ga wasu Musulmi fa! Haka batun yake ko a Turai, son rai da munafinci ke daidaita tunani game da duk wata kungiya da ta kunno kai domin sauya tunani, a addinance ko a siyasance! Saboda haka dangantakar kungiyar Boko Haram da Al’ka’ida ko alakanta Boko Akida da wayewar zamani ko Boko Sana’a da ruwa biyu a rayuwa, kamar yadda wasu ke yi a halin yanzu, shi ma ba sabon abu ba ne, kuma yana da dalili, babban dalilin kuwa bai wuce abubuwan da yawancin masu nazari ke ikirari ba ne. Akwai wata boyayyar manufa da wadannan kungiyoyi ke da su ko ake ganin suna da su, ko suke son cimmawa a kasar nan bisa tunanin ‘yan kungiyar ko na masu-iza-kantu-ruwa daga wani wuri can daban.

Ke nan matsalar Nijeriya da Arewa game da Boko Haram ko wasu sababbin kungiyoyi irin su a halin yanzu, ta wuce irin duk yadda ake tunani, matsala ce ta rashin son gaskiya da munafinci da son rai da rashin kishi da almundahana da mugun mulki da kyashi da karya da zamba-cikin-aminci. Matsala ce ta rashin kyakkyawan shugabanci da sata kiri-kiri daga wadanda aka dora wa alhakin ririta ‘yan dukiyar da Allah ya albarkace mu da ita.

Saboda haka ko mu yarda ko kada mu yarda, matsala irin ta Boko Haram  da kungiyoyi irin su da dama  ko ma wasu masu kama da ita za ta ci gaba da wanzuwa a kasar nan, in dai mun ci gaba da kasancewa cikin irin wannan tsarin na wake da shinkafa. Tsarin da bai san gabas ko yamma ko kudu ko kuma arewa ba. Duk tsarin da bai san mutunci da kara da sanin ya kamata ba, ba abin da zai haifar sai tashin hankali da tashin-tashina. Duk wani tsari da bai san kowa ba sai mai mulki, mai hannu-da- shuni, mai cuta da cutarwa, da ci da ceto da ci da addini, dole ya haifar da Boko Haram ko Mulki Haram ko Dukiya Haram ko Abuja Haram ko ma Nijeriya Haram!

Saboda gaskiyar magana ita ce, matsalar kasar nan matsala ce ta yin kemagas da duk wani ruhi na addini ko al’adu ko zamantakewar kwarai. Matsala ce ta rashi ga yawancin al’umma, alhali kuma wasu (‘yan kalilan) na faman yin kurme cikin tafkin wadata, kuma ba tsoron Allah, su fito su ce komi lami-kalau a cikin kasa!

Matsalarmu ta wuce ta Boko Haram ko Boko Akidah ko Boko Sana’a, duk kuwa da su ma matsala ce. Amma idan muna kallon yawan wadanda aka kashe ne daga hare-haren Boko Haram, ko kuma zaman dar-dar da muke fama da shi na rashin sanin makama ko katutun jahilci, to mun manta cewa milyoyin jama’ar kasar nan na ta faman mutuwa saboda talauci da yunwa da rashin kyakkyawan muhalli da faduwar gine-ginen bogi da rashin magungunan kiwon lafiya. Haka kuma nawa ke zaman dar-dar na rashin sanin inda abinci gobe zai fito? Nawa suke mutuwa kullum daga matattun titunan da muke da su ko kuma mata nawa ke mutuwa wajen haihuwa? Yara nawa ke mutuwa daga cututtukan da za a iya magance su? Nawa? Nawa ‘yan fashi da makami da sara-suka da eriya boyis suka kashe? Nawa? Ba sa misaltuwa!

Daga karshe nake cewa lokaci ya yi da za mu komo cikin hayyacinmu, mu fahimci inda muka fito da inda muke da kuma inda za mu. Inda muka fito da alama can ne wurin komawa, domin kuwa inda muke yanzu komi ya lalace. Can inda za mu kuma; nan kusa ko can nesa, ba mu da hasken abin da zai kasance. Sai dai muna iya hasashen inda za mu, musamman nan kusa, hoton kuma ba abin dadin kallo ba ne, domin kuwa harsashin da muka assasa na gina yau din na toka ne, ba zai dauki gini mai karko ba. Inda za mu can mai nisa kuwa, wannan ba a hannunmu ko hannun shugabanni da gwamnati ko hannun Boko Haram ko Boko Halal ko Boko Akidah ko Boko Sana’a take ba; hannun Allah ne, kuma muna alfahari da cewa shi da zai yi hisabi a wancan lokaci, adili ne, mai rahama ne, mai jin kai, kuma ba azzalumi ba ne!

Mun Kammala