Boko Haram: Abin da Gwamnan Borno ya kamata ya fahimta

Ina son wanan jarida mai albarka ta Aminiya ta ba ni dama in maida martani ga Gwanan Jihar Borno, Alahji Kashim Shettima a kan maganar da ya fada a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce: “Malamai ba sa iya caccakar Boko Haram.” Gwamna Kashim Shettima bai kamata ka fadi haka ba. Lallai tun a […]

Boko Haram: Abin da Gwamnan Borno ya kamata ya fahimta
Boko Haram: Abin da Gwamnan Borno ya kamata ya fahimta

Ina son wanan jarida mai albarka ta Aminiya ta ba ni dama in maida martani ga Gwanan Jihar Borno, Alahji Kashim Shettima a kan maganar da ya fada a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce: “Malamai ba sa iya caccakar Boko Haram.”

Gwamna Kashim Shettima bai kamata ka fadi haka ba. Lallai tun a shekara ta 2003 zuwa 2004 lokacin kana can kana fama da aikinka na banki a Zenith Bank malamanmu suke ta fadakarwa da jan hankali a kan wannan akida ta Khawarij (Boko Haram), wanda a wancan lokacin ana kiransu Yusufiyya.
Ba na mantawa, malami na farko da ya fara caccakar wannan tafiya a malaman Jihar Borno shi ne Sheikh Ali Mustapha; tun a farkon fari da kuma Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (Allah jikansa), wanda babu abin da bai fada ba a kan wannan tafiyar; wanda ba don Allah Ya sa ya fede gaskiya ba da Boko Haram sun kwashi kusan rabin matasan Ahulussunnan da ke cikin birnin Maiduguri.
Yallabai Gwamna, har wani kwamiti mai suna ‘AL-BALAGUL MUBEEN’ malamai suka kafa, domin caccakar wannan akida, wanda a kan wannan aikin ne Boko Haram suka kashe mana Sheikh Ja’afar a 2007. A kan caccakar Boko Haram aka kashe mana Sheikh Bashir Mustapha a 2010. A kan caccakar Boko Haram aka kashe mana Sheikh Ibrahim Abdullahi Ngomari da Sheikh Ibrahim Majimi da Sheikh Babagana Ibrahim, Shugaban Izala na Jihar Borno da kuma Sheikh Auwal Albani Zariya, ban da wadanda aka raba da gidajensu duk saboda caccakar wannan mummunar akidar.
Yallabai Gwamna, ya kamata ka dubi maganar da ka yi. Allah ka ba mu zaman lafiya.
Bilya Tukur Bakori (07030225194)

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50