Boko Haram: Amnesty ta zargi sojojin Kamaru da gallaza wa mutane
kungiyar Kare Hakkin Jama’a ta Duniya (Amnesty International) ta koka kan yadda ake tsananin gana wa mutane azaba a yaki da ayyukan ta’adanci na kungiyar Boko Haram a kasar Kamaru. Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis din makon jiya ta yi zargin cewa Ana gana wa wadanda aka tsare azaba da lakada […]
kungiyar Kare Hakkin Jama’a ta Duniya (Amnesty International) ta koka kan yadda ake tsananin gana wa mutane azaba a yaki da ayyukan ta’adanci na kungiyar Boko Haram a kasar Kamaru.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis din makon jiya ta yi zargin cewa Ana gana wa wadanda aka tsare azaba da lakada musu duka da azabtar da su ta hanyar nutsar da su a ruwa, yayin da wadansunsu azabat ta kai su ga mutuwa a wurare 20 da suka hada da sansanonin soja biyu da wasu sansanonin biyu da jami’an leken asiri ke kula da su da gidan wani da kuma wata makaranta.
kungiyar ta yi kira ga Amurka da sauran kawayenta na duniya su binciki jami’an sojinsu domin akwai yiwuwar suna da masaniya a kan azabtar da jama’a da aka yi.
Akwai daruruwan mutane a kasar Kamaru da ake zargi da goyon bayan kungiyar Boko Haram a mafi yawan lokuta ba tare da wata shaida ba, kuma jami’an tsaro na gana musu azaba, inji Amnesty.
kungiyar ta ce ta kafa hujja ce ta hanyar amfani da mutane masu yawa da suka ba da shaida da shaidun da aka samu na hotunan da tauraron dan Adam ya samar da wasu hotuna da shaidu na bidiyo, wajen fitar da rahoton mai taken “Dandalin azabtar da jama’a na kasar Kamaru: Take hakokin dan Adam da miyagun laifuffukan yaki a yaki da kungiyar Boko Haram.”
A yunkurin tsara rahoton a cewar kungiyar an tattara nau’ukan cin zarafi 101 na mutanen da aka tsare ba tare da bari a gansu ba, inda aka rika gana musu mummunar azaba a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017 a wurare fiye da 20.
“Mun yi ta nanatawa karara da yin Allah wadai da babbar murya kan miyagun laifuffukan yaki da kungiyar Boko Haram ta aikata a kasar Kamaru. Amma duk da haka babu dalilin da zai halatta aikata wannan mumunan aiki da jami’an tsaron Kamaru ke yi na gana wa al’ummar kasar mumunar azaba, mutanen da a mafi yawan lokuta akan kama su a tsare su ba tare da wata shaida ba, a sanya su fuskanci azabar da ta wuce kima,” inji Alioune Tine, Daraktan kungiyar Amnesty International mai kula da Shiyyar Afirika ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.
A watan Afrilun bana Amnesty ta ce ta rubuta wa mahukuntan kasar Kamaru wasika domin ba su kwafin abubuwan da ta gano a wannan rahoto, to sai dai babu wani martani da gwamnatin ta bayar, kuma ta ki yarda da dukan bukatun neman ganawa a kan batun.
kungiyar Amnesty ta yi kiyasin cewa daga shekarar 2014, Boko Haram ta kashe fiye da fararen hula 1,500 a Kamaru, tare da sace wadansu da dama.
Mutanen da aka gana wa azaba sun bayyana nau’oin azabtarwa 24 da aka gana masu, kuma daya daga cikinsu mai suna “akuya” ana daure hannuwansu a bayansu kafin a lakada musu duka. daya mai suna “lilo” ana sagale mutum ta hanyar sanya hanuwansa a baya yana lilo kafin a yi ta dukansa.
Kuma mafi yawan mutanen an gana musu azaba ne a wurare biyu: hedikwatar kai daukin gaggawa ta BIR da ke Salak kusa da arewacin garin Maroua da wani wurin da ke kusa da hedikwatar kasar wato Yaounde da ke karkashin sashin bincike na hukumar liken asiri ta Kamaru.