Boko Haram: An kashe maciji…!!!

Tun bayan bullowar kungiyar ‘Jama’atu Ahlus-Sunnati Lidda’awati Waljihad,’ wadda aka fi sani da Boko Haram a shekarar 2009, jama’a da dama musamman jami’o’i da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum suka dukufa wajen gano hanyoyin magance abubuwan da suka haddasa ayyukan ta’addanci Nijeriya – musamman Arewa maso gabas. Idan ba a manta ba, a […]

Boko Haram: An kashe maciji…!!!
Boko Haram: An kashe maciji…!!!

Tun bayan bullowar kungiyar ‘Jama’atu Ahlus-Sunnati Lidda’awati Waljihad,’ wadda aka fi sani da Boko Haram a shekarar 2009, jama’a da dama musamman jami’o’i da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum suka dukufa wajen gano hanyoyin magance abubuwan da suka haddasa ayyukan ta’addanci Nijeriya – musamman Arewa maso gabas. Idan ba a manta ba, a wajejen 2010 Jami’ar Bayero ta shirya wani taro, inda masana suka gabatar da makala mai taken ‘Daga Maitatsine zuwa Boko Haram,’ wannan makala ta yi bitar abubuwa  daban-daban tun daga kan abubuwan da suke haddasa Boko Haram daga tushe, tare da kokarin kawo hanyoyin magance aukuwar abin a nan gaba. Haka nan tsohon Shugaban kasa Dokta  Goodluck Ebele Jonathan ya kafa kwamiti a karkashin shugabancin Alhaji Usman Galtimari, wanda ya mika rahotonsa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Arch. Muhammad Namadi Sambo a ranar 26 a watan Satumba, 2012. Daga bisani gwamnatin tarayya ta kara kafa wani kwamitin a karkashin jagorancin tsohon Ministan harkokin cikin gida, Alhaji Abba Moro akan ya yi nazarin shawarwarin da kwamitin Galtimari ya bayar, sannan ya bai wa gwamnati shawara akan yadda za ta yi amfani da su.
 A matakin malaman addinai kuwa, mutane irin su Marigayi Sheikh Ja’afar Adam da Marigayi Sheikh Muhammad Auwal (Albanin Zariya), (Allah ya jikansu da rahama) da Dokta Ali Isa Pantami da Bishop Mathew Hassan Kuka da ‘Cardinal’ John Oneyekan da sauransu, dukkansu sun yi kokari wajen fito da matsalar Boko Haram fili, tare da kokarin kawo dalilan da suka haddasata, tare da bayar da shawarwarin da suke gani idan hukuma ta dauka za su taimaka wajen shawo kan al’amarin.
Su kuwa malaman Musulunci, sun fi alakanta abin da son shahara (Hubbiz Zuhur) da karancin fahimtar addini da karsashin matasa (hamasa) da kuma talauci da ya yi wa al’ummar Arewa katutu. Su kuwa  Malaman addinin Kirista sun fi ta’allaka abin da amfani da ‘yan siyasa suke yi da addini don cimma wata bukatar siyasa, inda suka rika yawan bayar da misali da yadda a shekarar 2000 jihohi irin su Zamfara da Kano da Kaduna da Bauchi da sauransu suka shelanta kaddamar da Shari’ar Musulunci ga talakawa! A yayin da gefe guda hakan bai hana su facaka da wawure kudin gwamnati ba!
Bayan rantsar da Shugaba Muhammad Buhari a ranar Juma’a 29 ga watan Mayu, 2015, ya mayar da tsaro daya daga cikin kudurori uku da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai. Tun a watan farko da hawan mulkinsa ya ziyarci kasashen Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Benin don ganin an hada karfi da karfe wajen yakar Boko Haram. Sannan duk lokacin da ya tsinci kansa a wajen wani taro sai ya mika kokon barar Najeriya wajen tallafa mata wajen yaki da ta’addanci. Kwalliya kuwa ta biya kudin sabulu, domin a halin yanzu sojojin Najeriya a karkashin jagorancin Manjo-Janar Tukur Buratai sun ci karfinsu. Amma wani abin lura, shi ne, kamar gwamnati ta yi biris da shawarwarin da masna suka bayar ba.
Manufata, ita ce,  fito da wadannan matsalolin fili tare da kokarin ganin an magance matsalar Boko-Haram ko kuwa dai da sauran rina a Kaba?  To, idan haka ne ina mafita? A nan na kawo wasu bangarorin da suke tunanin ya kamata gwamnati da al’umma sun ba su kulawa ta musamman don ganin an fitar da A’i daga rogo;
Na daya,  idan muka duba za mu ga cewa malamai suna da gagarumawar rawar da za su taka wajen yakar wannan matsalar, musamman kasancewarsu ‘Magada Annabawa,’  kuma su ked a alhakin saiszaita tunanin al’umma.  Babban aikin su na farko, shi ne, su fahimtar da dalibansu cewa,’ Musulunci gamammen tsari ne da ya shafi daukacin bangarorin rayuwa baki daya, sannan neman na kai ne da wadata (ba kasala da zaman kashe wando ba), kuma tsari ne da ya dace da kowane zamani.’ Idan mutane sun fahimci wannan sai a karantar da su tarihin Annabi Rahama, tsira da Aminci su kara tabbata a gare shi, da yadda ya zauna da wadanda ba Musulmi ba.  Sai dai abin haushi ne ka ga malamin da yake da’awar gadon Annabta, amma kullum kokarinsa ya cusa wa mabiyansa kyama da kallon hadarin kaji ga duk wanda ba ya bin irin fahimtarsa. To, idan mutum bai mutunta fahimtar wadanda suke addini guda ba, gaya mini ta yaya zai girmama fahimtar wanda kwata-kwata ba addinin su daya ba? Ko kuma ka ga malami ya tara talakawa bayin Allah, yana ta zayyana musu yadda jami’an gwamnati suke badakala da kudin al’umma ba tare da kawo musu mafita ba, alma’arin da ke nuni da kwarewa wajen kawo matsala, amma ba ma tunanin mafita daga cikinta, wanda wannan abin shi yake tasiri a duk lokacin da aka samu wani mai mummunar fahimtar haramta Boko da aikin gwamnati, sai irin wadannan mutanen su bi shi.
Na biyu, game da makarantun allo (Tsangaya), a nan zai fi kyau mu koma ga tarihin yadda aka kafa wadannan makarantu, kuma masu hankalin cikinmu su yi mana nazari da tunani mai zurfi  kan ko muna bukatar irin wannan tsarin (na makarantun allo) a karni na 21? Shin daidai ne mu turo yara masu kananan shekaru su yi ta gararamba a kan titunan birane? Ko wannan ce hanya kadai da za mu koyar da ’ya’yanmu addini? Shin koyarwar Musulunci ce mu bar ‘ya’yanmu cikin kazanta da annakiya?!
Lokacin da Luggard ya yi tunanin canza harkokin gudanarwa yayin da ya ga tasirin Tsangaya a kasar Hausa da tunanin rusa ta, don kafa kishiyarta a garin Bidda ta koyar da karatun zamani, kuma ya dauki malaman Alkur’ani daga cikin Nufawa ya ci gaba da koyar da su, ana ba su alawus na sule guda a wata. Ya fara daukar wannan mataki ne bayan ya sa an yi masa kididdigar makarantun tsangayun Arewa da bincike domin sanin hanyar da zai bullo musu a shekarara 1904, inda alkaluma suka nuna cewa, yawan tsangayun (a Arewa) ya kai dubu 25, yawan almajiransu kuma ya kai dubu dari 250 a wancan lokaci. Amma yanzu binciken da Gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau tasa aka gudanar a tsakanin 2003  zuwa 2007 ya nuna muna da almajirai guda miliyan uku da dubu dari 4 da981!!!.
Wannan adadin ya dada zaburara da Lugard wajen yada  ilimin zamani aBidda) da larduna, inda ya kafa makarantun midil-midil, domin koyar da ‘yan kasa harshen Turanci da al’adun Bature da kuma yi wa tsangayu kafar angulu, wanda ya kai su ga halin da suke ciki a yau!.
Ita kuwa gwamnati ta ki ci gaba da daukar nauyin abin dari bisa dari (kamar yadda Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta fara).
Na uku, mummunan talauci ne ya bai wa Boko Haram gindin zama a Arewa maso Gabas. Don haka ko an yi maganin Boko Haram idan ba a kawar da talauci ba, to, ba a yi komai ba, tamkar an kashe maciji ne ba a sare kansa ba. Dole ne a fuskanci matsalar da ke damun talaka da yanayin rayuwa kafin a ce an samu nasara. Gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su fito da wani shiri da zai magance kuncin rayuwar da talaka yake ciki, domin shi ma ya san ana yi da shi.
A nan ina bai wa gwamnatin tarayya shawara da ta tattara rahotanni da makalolin da aka gabatar  kan sabubbuban aukuwa Boko Haram. Su kuwa Gwamnatocin Jihohin Arewa, su yi nazarin dabarun zamanantar da Makarantun Tsangaya kamar Makarantun Madinatul Ahbab na Marigayi Sheikh Haruna Rasheed Fagge (RA) da Makarantun Gwani Salihu dan Zarga (Allah ya ji kansa da rahama), da Makarantun Maulana Sheikh dahiru Usman Bauchi da dai sauransu. Sannan (gwamnati) ta samar da hanyoyin magance talauci, a kulla alaka ta kut-da-kut da malaman addini domin su taya su saita tunanin al’umma.
Gwamnati ta sani cewa, matukar ba ta yaki talauci da zaman kashe wando a kasa (musamman Arewa) ba, to, Boko Haram na nan daram! Idan ma a halin yanzu an kakkabeta, tare da kwato dukkanin kananan hukumomin da suke a karkashinsu, to, wasu (Boko Haram din) za su iya tasowa nan gaba, kamar yadda lamarin ya kasance sananne, cewa, Maitatsinen da aka yi a tsakanin shekarun 1982 zuwa 83 yana da alaka ta kusa ko ta nesa da Boko Haram a yau. Allah ya ba mu dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali, Ya ba mu shugabanni masu hangen nesa. Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya. Amin  
Maibiskit, daliba ce a sashen koyon aikin jarida na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano (Kano Polytechnic) [email protected]  0809 470 7758 (Tes kawai don Allah).

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya