Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa
Harin wanda ya fara daga misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, kuma ya ɓarnata dukiyoyi a tsakiyar daren.

Wasu gungun ‘yan Boko Haram ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki cikin dare a garin Kwapre da ƙauyukan da ke gundumar New Yadul a ƙaramar hukumar Hong a Jihar Adamawa.
Harin wanda ya fara daga misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, kuma ya ɓarnata dukiyoyi a tsakiyar daren.
- Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza
- Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno
Al’ummar yankin sun ce, an ƙona wuraren ibada da makarantu da gidaje da wuraren kasuwanci, sannan an wawushe dukiyoyi na miliyoyin Naira.
Mista Joel Kulaha, Hakimin garin Kwapre da Abalis Jawaja, kuma dagacin ƙauyen, ya ce maharan sun farwa al’ummar garin, inda suka ƙona gine-gine tare da kwashe kayayyaki masu daraja.
Sun ce, an yi sa’a ba a rasa rayuka a harin ba, domin mazauna yankin sun yi gargaɗin ƙaruwar barazanar harin, sun tsere daga gidajensu kafin maharan su iso.
“Mun tsere da rayukanmu, amma duk abin da muka mallaka ya tafi,” kamar yadda Kulaha ya koka, yana kwatanta harin da aka kai.
An samu rahoton cewa dakarun sojin da ke kusa da Garaha sun mayar da martani kan harin da sanyin safiya, inda suka fatattaki maharan.
Sai dai mazauna yankin sun ce matakin sojan ya makara ne domin daƙile ɓarnar da ta ɓarke ƙauyukan.