Boko Haram: An rufe makarantu 136 a Kamaru
A shekaranjiya Laraba ne Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru suka ce an rufe makarantu akalla 136 a cikin kasar saboda hare-haren ‘yan Boko Haram.Makarantun da aka rufe sun haxa da na firamare da na sakandare, kamar yadda BBC ta bayyana.Galibin makarantun suna yankuna takwas ne a lardin Arewa-Mai-Nisa, inda ‘yan Boko Haram ke tafka ta’asa.Yawancin makarantun, […]
A shekaranjiya Laraba ne Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru suka ce an rufe makarantu akalla 136 a cikin kasar saboda hare-haren ‘yan Boko Haram.
Makarantun da aka rufe sun haxa da na firamare da na sakandare, kamar yadda BBC ta bayyana.
Galibin makarantun suna yankuna takwas ne a lardin Arewa-Mai-Nisa, inda ‘yan Boko Haram ke tafka ta’asa.
Yawancin makarantun, kamar waxanda ke kauyen Kerawa – ana amfani da su ne a matsayin sansanonin ‘yan gudun hijirar Najeriya waxanda suka tsallaka cikin Kamaru.
Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun ce ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe kimanin mutane 1,200 a kasar tun daga shekarar 2013.