Boko Haram: An sake tura ‘yan sanda dubu 2 a Arewa maso Gabas
Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya (IGP) Ibrahim Idris ya bayar da umarnin tura karin ‘yan sanda dubu biyu yankin Arewa maso Gabas don dakile ayyukan ta’addanci, an tura jami’an tsaron ne tare da karnukan tsaro da nufin taimaka wa rundunar sojojin Operation Lafiya Dole wajen yakar Boko Haram. Kakakin Hukumar ‘yan sandan DCP Jimoh […]
Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya (IGP) Ibrahim Idris ya bayar da umarnin tura karin ‘yan sanda dubu biyu yankin Arewa maso Gabas don dakile ayyukan ta’addanci, an tura jami’an tsaron ne tare da karnukan tsaro da nufin taimaka wa rundunar sojojin Operation Lafiya Dole wajen yakar Boko Haram.
Kakakin Hukumar ‘yan sandan DCP Jimoh Moshood ya ce, tura ‘yan sandan yankin ya yi daidai da sashi na 4 na dokar hukumar ‘yan sandan Najeriya.