Boko Haram: An yi mana binciken kwakwaf -Wadanda aka sako

Babban Hafsan Sojan Najeriya Manjo Janar Kenneth Minimah, ya bayar da uamarnin sakin wadansu mutane 182, wadanda ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne kuma aka kame su a lokutan baya a Makiduguri. Babban Hafsan Sojan ya bayar da umarnin sakin ne a yayin bikin tunawa da ‘Yan Mazan jiya wadanda suka kwanta dama, da […]

Boko Haram: An yi mana binciken kwakwaf -Wadanda aka sako
Boko Haram: An yi mana binciken kwakwaf -Wadanda aka sako

Babban Hafsan Sojan Najeriya Manjo Janar Kenneth Minimah, ya bayar da uamarnin sakin wadansu mutane 182, wadanda ake zargin ‘Yan kungiyar Boko Haram ne kuma aka kame su a lokutan baya a Makiduguri.

Babban Hafsan Sojan ya bayar da umarnin sakin ne a yayin bikin tunawa da ‘Yan Mazan jiya wadanda suka kwanta dama, da aka gudanar da shi a garin Maiduguri. Inda ya yi nuni da cewa rundunar sojan ta yi bincike sosai a kan kowane mutum cikin su 182 din sai ta gano cewa ba su da laifi. A cikin 182 din akwai mata 45 da yara masu kananan shekaru 25, sai kuma jarirai. Rundunar ta kuma mika wadannan mutanen ga gwamnatin jihar Borno.
Wani matashi mai suna Abubakar Ibrahim, ya shaida wa wakilinmu cewa ‘’Ni ina cikin Unguwarmu ce ta Gwange, na fito daga gida sai kawai Sojoji suka kama ni suka sanya ni a cikin mota suka kawo ni barikinsu, yau watanni 9 ke nan. Ni kuma shekaruna 15 ne. Sojojin sun kula da mu, suna ba mu abinci a kullum sau 3, kuma muna yin wanka kullum. Amma a yanzu ina cikin farin ciki saboda ba su same ni da laifin komaiba kuma sun sake ni a yau.’’
Shi ma Malam Bakura Modu, bayyana wa Aminiya ya yi cewa, ‘’Ni ina zaune ne a Unguwarmu sai Sojoji suka yi kame, ciki kuwa har da ni, suka kaimu barikinsu suka tsare mu har tsawon shekara daya suna bincikanmu, amma ba su same mu da laifi ba, ga shi kuma Allah Ya sa suka sake mu. A gaskiya na yi farin ciki. Ni yau shekaruna 55, kuma ina da mata biyu da yara 6, sannan duk da cewa sun kama mu sun kai mu barikinsu, amma a gaskiya ba su musguna mana ba har zuwa wannan lokacin da suka sake mu bayan da suka kammala bincikanmu.’’
Ita kuwa Malama Rukayya Abdullahi, cewa ta yi, ‘’Ni an kama ni ne saboda an kashe mijina wai an ce shi dan Boko Haram ne, alhali kuma karya ne, ka ga ke nan an yi mini sharri ke nan, kuma yau watana 9 ke nan ina kulle, kodayake dai suna kula da mu har tsawon wannan lokaci, amma ba a son raina ne na kasance a wannan wuri ba. Sun kuma yi mana binciken kwakwaf ta yadda dole sai ka fadi tarihinka da komai na gidanku, amma dai a yau ga shi sun sake mu kuma ina mai godiya ga Allah da suka sake mu. Suna ba mu abinci sau 3 a rana, kuma muna wanka a kullum, saboda haka mun gode musu.
Malama Hajara kuwa wanda ta haifi Jariri a lokacin da take garkame cewa ta yi, ‘’Ni sun kama ni ne da cikin wata daya bayan da aka kashe mijina, amma sun taya ni rainon cikina, domin kuwa suna kai ni Asibitinsu, kuma suna ba mu abinci a kowane lokaci. Amma bayan da na haihu sun yi mini binciken kwakwaf, kuma babu wani abu da suka yi mini na musgunawa, har zuwa wannan lokacin da suka sake mu, kuma muna gode wa Allah, muna gode musu.’’
Shi kuwa Babagana wanda yaro ne da bai wuce shekara 7 ba, cewa ya yi, ‘’Ni ban san abin da na yi aka kawo ni nan ba, amma wai sun ce ni Boko Haram ne, ni kuma ba Boko Haram ba ne, domin na dawo makaranta ne suka dauke ni, Mamata da Babana duk ba su sani ba, ni yanzu shekarata 7ne, kuma watannina 9 a nan, amma ba su taba dukanaba, sai dai suna yawaita tambayata, amma kuma suna ba mu abinci a kullum har sau 3, kuma muna yin wanka a kullum, sannan idan ba ni da lafiya sukan ba ni magani, har ma wani lokaci su kaini asibitinsu. Sai dai kuma duk da haka ban so in shiga wannan wuri ba, na so a ce an bar ni na ci gaba da karatuna kuma ina tare da iyayena. Amma Alhamdulillahi tun da sun sake mu, yanzu zan tafi wajen iyayena in kuma ci gaba da karatuna.’’