Boko Haram: An yi wa wadanda yaki ya jikkata ruwan nairori a Abuja
Gidauniyar neman gudunmawa don tallafa wa wadanda yaki ya jikkata a jihohin Arewa maso Gabas da kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya kafa ya samu Naira miliyan 230 a yayin kaddamar da gidauniyar a Abuja a jiya Alhamis.Gudunmawa mafi tsoka ta fito ne daga fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Aliko dangote wanda gidauniyarsa […]
Gidauniyar neman gudunmawa don tallafa wa wadanda yaki ya jikkata a jihohin Arewa maso Gabas da kamfanin buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya kafa ya samu Naira miliyan 230 a yayin kaddamar da gidauniyar a Abuja a jiya Alhamis.
Gudunmawa mafi tsoka ta fito ne daga fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Aliko dangote wanda gidauniyarsa ta Gidauniyar Dangote ta bayar da Naira miliyan 100. Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas sun bayar da Naira miliyan 60, wato Naira miliyan goma-goma kowaccensu.
Kamfanin Daily Trust da ya shirya gidauniyar ya bayar da Naira miliyan goma, yayin da ’yan Majalisar Wakilai da suka fito daga yankin Arewa maso Gabas suka bayar da Naira dubu 500 kowannensu, inda jimilla ta zama Naira miliyan 22.
Bankin JAIZ ya bayar da naira miliyan biyar, sai Kamfanin Bunkasa Zuba Jari na jihohin Arewa (NNDC), Naira miliyan biyar, sai toshon Gwamnan mulkin soja na tsohuwar Jihar Kano, Kanar Sani Bello, Naira miliyan biyu.
Wadanda suka bayar da Naira miliyan daidai sun hada da tsohon Ministan Shari’a Alhaji Abdullahi Ibrahim (SAN) da Alhaji Suleiman Yahya da Alhaji Bature Masari da Kamfanin NAHCO da wani da ya nemi a boye sunansa da kuma kamfanin buga jaridar The Sun a karkashin shugabancin tsohon Gwamnan Jihar Abiya Mista Orji Uzor Kalu. Wadanda suka bayar da rabin miliyan sun hada da Kamfanin H&M da Alhaji Garba Ahmad, sai tsohuwar Ministar Ilimi Dokta Oby Ezekweseli wadda ta bayar da Naira dubu 200.
Tunda farko a jawabin shugaban taron kuma shugaban Bankin Jaiz Alhaji Umaru Mutallab ya yaba wa kamfanin Daily Trust kan wannan hobbasa da ya yi domin tallafa wa wadanda ricikin Boko Haram ya shafa tare da tagayyara su jihohin Arewa maso Gabas.
Ya ce, Annabi Muhammadu (SAW) ya ce “Imaniin dayanku ba ya cika sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa.” Don haka ya bukaci jama’a su tallafa don sama wa wadanda suka tagayyara abinci da sana’o’i da samar musu da abin dogaro don a gudu tare a tsira tare.
Taron ya sami halartar gwamnonin jihohin Borno da Adamawa da Bauchi da sauran manyan mutane da dama daga sassan kasar nan.