Boko Haram: Attahiru mai fada da cikawa ne —Zulum
A wata hudu Janar Attahiru ya je Borno sau shida don kara wa sojoji kaimi.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ce Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya nuna a aikace cewa zai yi duk mai yiwuwa wurin murkushe kungiyar Boko Haram.
Zulum ya ce daga nada Jannar Attahiru a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasa a watan Janairu zuwa rasuwarsa a watan Mayu, ya tsaya kai da fata a yaki da kungiyar, inda sau shida yana zuwa Jihar Borno domin ganin sojoji da kama musu kwarin gwiwa a yaki da kungiyar.
- Jana’izar Janar Attahiru: Yadda Gwamnoni suka fusata ’Yan Najeriya
- An yi wa Buhari ca kan rashin halartar jana’izar Janar Attahiru
“Jajircewarsa a yaki da Boko Haram a fili ta ce. Cikin dan lokacin da aka nada shi ya ziyarci Jihar Borno sau da dama, yana ganawa da kwamandoji da sojojin da ke bakin daga — a-kai-a-kai yana kara musu azama,” inji Zulum.
Ya ce tsayuwar dakar da marigayi Janar Attahiru ya yi domin kawo karshen ayyukan ta’addanci ta nuna a bayyana cewa shi mutum ne mai fada da cikawa.
Ya ce a lokacin ziyarar, Janar Attahiu kan bi sansanonin soji inda yake kara wa dakarun da ke bakin daga kaimi a aikin da suke yi na samar da tsaro da aminci.
Gwamnan Bornon ya bayyana haka ne ranar Asabar tare da magabacinsa, Sanata Kashim Shettima a wurin jana’izar marigayi Janar Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama a ranar Juma’a.
“Mutanen Borno na godiya a gareshi da sauran dakarun da suka kwanta dama a fagen fama bisa gudunmawarsu mara adadi ga Jihar Borno da kuma Najeriya baki daya,” inji shi.