Boko Haram ba reshe ne na Alka’ida ba – Amurka
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram ba reshe ne na kungiyar Alka’ida da ta addabi duniya da ta’addanci ba.A ranar Asabar da ta gabata ce, a wajen wani taro kan tsaro a kasar Faransa, Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya bayyana kungiyar Boko Haram da “Alka’idar Afirka ta Yamma.” Sai dai kamfanin dillancin […]

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram ba reshe ne na kungiyar Alka’ida da ta addabi duniya da ta’addanci ba.
A ranar Asabar da ta gabata ce, a wajen wani taro kan tsaro a kasar Faransa, Shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan ya bayyana kungiyar Boko Haram da “Alka’idar Afirka ta Yamma.”
Sai dai kamfanin dillancin labarai na AP ya ce, Amurka ta ce duk da cewa kungiyoyin ’yan ta’adda a sassan duniya an san suna da alaka, ta yi gargadin a tunkari Boko Haram a matsayin “kungiyar ’yar ta’addar kanta.”
Wani bayani da karamar Jakadar Amurka a Najeriya Wendy Sherman ta karanta wa manema labarai a Legas a ranar Litinin da ta gabata ya zo ne a daidai lokacin da aka kammala taron tsaro da Shugaban Faransa Francois Hollande ya dauki nauyi a Paris a ranar Asabar.
Sherman, wadda ta yi magana tare da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, mai kula da harkokin Afirka, Linda Thomas-Greenfield da ko’odinetar yaki da ta’addanci ta ma’aikatar wajen Amurka, Tina Kaidelow, ta ce ana sa ran cikin wannan mako Majalisar dinkin Duniya ta kakaba wa Boko Haram takunkumi.
Ta ce, “Boko Haram kungiyar ta’adda ce mai zaman kanta, kuma Amurka ta ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar ta’adda ta kasar waje. A wannan zamani zai yi wuya wata kungiyar ta’adda ta rasa alaka da wasu kungiyoyin komai kashinta. To amma mun dauki Boko Haram a matsayin kungiyar ta’adda mai zaman kanta. Lokacin da Majalisar dinkin Duniya ta sanya mata takunkumi, za ta kwace kadarorinta, ta hana jami’anta tafiye-tafiya da sauran ayyuka. Ya danganta kan yadda aka ayyana. Kuma ina jin wannan zai faru cikin sauri. Cikin sauri, domin zai yi wahala a samu kasar da ba za ta goyi bayan haka ba.”
Sherman ta kara da cewa Amurka za ta tallafa wa gwamnatin Najeriya wajen ganin an dawo da ’yan matan Chibok da ransu. Ta ce, ’yan matan makaranta da aka sace sun zama “na duniya ba na Najeriya kawai ba.” Kuma ta ce ana yin duk kokarin da ya wajaba don tabbatar da Afirka ta Yamma ba ta zama wurin kyankyasar ’yan ta’adda ba.
Ta nanata cewa al’ummar “ba za su sanya sojojinsu a fafatawa” a Najeriya don ceto ’yan matan ba, inda ta ce, za a bayar da tallafi ne na bayanan sirri kawai. Sai kuma tallafin horo na musamman da za ta ba sojojin Najeriya don ceto ’yan matan idan bukatar haka ta taso.
A nata bangare, Thomas-Greenfield, ta ce Amurka tana tsara wani yunkuri na ceto ’yan matan tare da hadin gwiwar sauran kasashe. “Kuma Najeriya ta ba da wani babban jami’i da shi ne za su rika tuntuba tare da aiki da shi kafada da kafada,” inji Thomas-Greenfield. Al-
Ita kanta kungiyar Alka’ida ta nuna kaduwarta das ace ’yan matan da kungiyar Boko Haram ta yi, inda ta ce hakan wani yunkuri ne na bata sunan mujahidai kamar yadda jaridar New York Timse ta Amurka tta kalato daga kafar sadarwar intanet ta kungiyar.
kungiyoyin Musulmi da jihadi da dama suna nesanta kansu da Boko Haram, inda hatta mutanen da aka sani da tsaurin addini suka yi fatar wadanda suka sace ’yan matan za su dubi Allah su sako su kamar yadda Musulunci ya tanada.
Alka’ida dai ta sha gargadin magoya bayanta su guji kai hari ka fararen hular da ba su san hawa ko sauka ba, abin da kungiyar Boko Haram take aiwatarwa kan talakawan kasar nan, kamar yadda jaridar ta ce.