Boko Haram: Bankin Duniya zai taimaka da dala biliyan 2
A shekaranjiya Laraba ne Bankin Duniya ya sha alwashin kashe dala biliyan biyu da miliyan 100 wajen sake gina yankin Arewa-maso-Gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya daidaita, kamar yadda BBC ta bayyana.Wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar, ta ce matakin ya biyo bayan tattaunawar Shugaba Buhari da gidauniyar Bill and […]
A shekaranjiya Laraba ne Bankin Duniya ya sha alwashin kashe dala biliyan biyu da miliyan 100 wajen sake gina yankin Arewa-maso-Gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya daidaita, kamar yadda BBC ta bayyana.
Wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar, ta ce matakin ya biyo bayan tattaunawar Shugaba Buhari da gidauniyar Bill and Melinda Gates da kuma Bankin Duniya da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya-WHO a birnin Washington.
Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya ce sake gina matsugunan mutane kusan miliyan daya da ‘yan Boko Haram suka raba da muhallinsu na daga cikin abubuwan da ya fi bai wa mahimmanci a gwamnatinsa.
A bisa tsarin dai, Bankin Duniya zai kashe wannan kudin ne ta hannun Cibiyar Raya kasashen Duniya wadda ke ba da bashi ga gwamnatoci a kudin ruwa mara yawa. Shekaru 10 na farko, zai kasance babu kudin ruwa sai kuma kudin ruwa mara yawa a shekaru 30 masu zuwa. Bankin Duniya din kuma ya ce zai kashe kusan dala miliyan 300 a allurar rigakafi kan cutar Maleriya. A yayinda gidauniyar Bill and Melinda Gates tare da hadin gwiwar Gidauniyar dangote domin kawar da cutar Polio daga Najeriya.