Boko Haram: Buhari ya nuna damuwa kan amfani da sojan haya

Zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yadda kasar nan ta dogara da sojojin haya daga kasar Afirka ta Kudu a yakin da ake yi da Boko Haram. Muhammadu Buhari ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya bayyana da gazawar sojojin Najeriya wajen kare rayuka da dukiyar al’umma. Buhari wanda […]

Boko Haram: Buhari ya nuna damuwa kan amfani da sojan haya
Boko Haram: Buhari ya nuna damuwa kan amfani da sojan haya

Zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan yadda kasar nan ta dogara da sojojin haya daga kasar Afirka ta Kudu a yakin da ake yi da Boko Haram.

Muhammadu Buhari ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya bayyana da gazawar sojojin Najeriya wajen kare rayuka da dukiyar al’umma. Buhari wanda zai karbi ragamar mulki a ranar 29 ga Mayun nan ya ce akwai bukatar ’yan Najeriya su koyi rayuwa gwargwadon samunsu.
Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne lokacin da shugabannin kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) suka kai masa ziyara a Kaduna, inda ya nanata cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da bin ka’ida wajen sarrafa dukiyar jama’a tare da magance matsalar tsaro da magance rashin aikin yi da cin hanci da rashawa.
Zababben Shugaban kasar ya ce: “Sojojin Najeriya ba su taba nuna gazawa irin wannan lokaci ba, sojoji ne da ba za su iya kare kananan hukumomi 14 daga cikin 774 da ke kasar nan ba. Don haka gwamnatina za ta mayar da hankali kan manyan abubuwa uku idan ta kama aiki, wato rashin tsaro da tattalin arziki rashin aiki cin hanci. Za mu tabbatar mun kai rashin tsaro cikin kabari.”
Muhammadu Buhari ya kara da cewa: “Sojojin Najeriya sun kasa yin kaanan abubuwa, sai da suka kawo sojojin haya daga Afirka ta Kudu kafin su samun nasarar baya-bayan nan a Arewa maso Gabas. Ban san ku nawa kuka san wannan ba; ’yan kwanakin da suka gabata na samu labarin cewa, nasarar da aka samu a Arewa maso Gabas ta samu ne saboda sojojin haya daga Afirka ta Kudu da aka yi amfani da su.”
Buhari ya yi alkawarin za a karfafa gwiwar sojoji da jami’an tsaro tare da kula da dubban mutanen da Boko Haram suka raba da muhallinsu.
Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar mutane suna rayuwa gwargwadon samunsu, “Ba za mu lamunci yanayin da mutane za su rika facaka fiye da samunsu ba,” inji shi.
Ya ce tsarin jam’iyyu da dama ya fi dacewa, domin duk jam’iyyar da ta gaza za a iya yin waje da ita.
Shugaban kungiyar ACF, Alhaji Ibrahim Ahmadu Coomassie ya bukci Buhari ya magance manyan matsalolin Najeriya. “Matsayin da aka kai na lalacewar kyawawan dabi’u da cin hanci da rashawa da aikata miyagun ayyuka da rashin aikin yi a tsakanin jama’a da yunwa musamman a tsakanin mutanen karkara da kuma rashin damuwa da rayukan dan Adam ba a taba ganin irin na shekara shida da suka gabata ba,” inji shi.
Coomassie ya ce mayakan Boko Haram sun lalata Arewa maso Gabas, sannan rashin wutar lantarki suna ci gaba da kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasa.
Ya ce tsarin fifita mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya da na Shugaban Ma’aikata a kan na ministoci wajen girma ya saba wa ka’idar tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da aikin gwamnati.