Boko Haram: Buhari zai yi taro da shugabannin yankin Tafkin Chadi yau
Shugaban Najeriya Muhammadu zai yi wani taro don ganawa da shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi su shida a yau Alhamsi, a cikin shugabannin harda shugaban kasar Chadi Idriss Deby wanda za a yi a N’Djamena babban birnin Chadi kan batun Boko Haram. Shugaba Buhari ne zai jagoranci taron a matsayinsa na shugaban gwamnatin kasashen yankin […]
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu zai yi wani taro don ganawa da shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi su shida a yau Alhamsi, a cikin shugabannin harda shugaban kasar Chadi Idriss Deby wanda za a yi a N’Djamena babban birnin Chadi kan batun Boko Haram.
Shugaba Buhari ne zai jagoranci taron a matsayinsa na shugaban gwamnatin kasashen yankin tafkin Chadi, kamar yadda mai taimaka wa Shugaban akan watsa labarai Femi Adesina ya sanar.
Ana saran taron zai sake duba batun yanayin tsaro a yankunan da rikicin Boko Haram ke shafa, da kuma inganta Rundunar Hadin Gwiwa ta kasa da kasa don ceto yankin daga halin da yake ciki.