Boko Haram ce ta bakwai wajen kudi a kungiyoyin ’yan ta’adda na duniya

An bayyana kungiyar Boko Haram da ke Najeriya a matsayin ta bakwai wajen kudi a tsakanin kungiyoyin ’yan ta’adda na duniya.Jaridar Nigerian Tribune ne ta ruwaito haka daga mujallar The Richest, wadda ta ce kudin da maharan kungiyar suka samu daga shekarar 2006 zuwa 2011 ta hanyar karbar kudin fansa daga garkuwa da mutanen da […]

Boko Haram ce ta bakwai wajen kudi a kungiyoyin ’yan ta’adda na duniya
Boko Haram ce ta bakwai wajen kudi a kungiyoyin ’yan ta’adda na duniya

An bayyana kungiyar Boko Haram da ke Najeriya a matsayin ta bakwai wajen kudi a tsakanin kungiyoyin ’yan ta’adda na duniya.
Jaridar Nigerian Tribune ne ta ruwaito haka daga mujallar The Richest, wadda ta ce kudin da maharan kungiyar suka samu daga shekarar 2006 zuwa 2011 ta hanyar karbar kudin fansa daga garkuwa da mutanen da suka sace ya kai Dala miliyan 70, (kimanin Naira biliyan 11 da miliyan 550).
kungiyar da ta zo ta daya ita ce ta ISIS da ke kasashen Siriya da Iraki wadda aka ce kudin da ta samu daga satar makamai da fashi a bankuna sun kai Dala biliyan biyu sai kungiyar IRA ta kasar Ireland mai Dala miliyan 450 da ake zargin samu ne ta hanyar kudaden sata, yayin da Taliban ta zo ta uku da Dala miliyan 400 da ake zargi ta samu ta hanyar safarar miyagun kwayoyi da fataucin mutane da kwace da kuma tallafi daga wasu kungiyoyin kasashen waje.
kungiyar Alka’ida ce ta zo ta hudu da Dala miliyan 100, yayin da mayakan ’yan Gurguzu na FARC da ke kasar Kolombiya ta zo ta biyar da Dala miliyan 80 zuwa miliyan 350.
kungiyar Lashkar-e-Tayyiba da ke Pakistan ce ta zo ta shida da aka ce tana samun Dala miliyan 100 a shekara.