Boko Haram: Chadi ta tsawaita wa’adin dakarunta a Najeriya
A shekaranjiya Laraba ne majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da tsawaita wa’adin dakarun kasar a yakin da suke da Boko Haram har sai lokacin da aka sami nasara a yakin. Sai dai wasu jam’iyyun adawa na kasar Chadin sun ki amince wa da matakin suna masu bukatar cikakkun bayanai kan adadin kudaden da za […]
A shekaranjiya Laraba ne majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da tsawaita wa’adin dakarun kasar a yakin da suke da Boko Haram har sai lokacin da aka sami nasara a yakin.
Sai dai wasu jam’iyyun adawa na kasar Chadin sun ki amince wa da matakin suna masu bukatar cikakkun bayanai kan adadin kudaden da za a kashe da kuma dakarun da za a tura.
kasar Chadi dai ta bayar da gudunmawar sojoji 2,500 a yakin da Najeriya da makwabtanta ke yi da mayakan Boko Haram.
Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyin jama’a da gidajensu a tsawon shekaru shida.
Har ila yau, a farkon watan nan ne Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya ce rashin aiki tare tsakanin dakarun Najeriya da na Chadi, shi ya sa aka kasa damke Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau. Dakarun Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma jamhuriyar Nijar ne ke yaki da kungiyar Boko Haram.