Boko Haram: Fararen hula 10,000 sun mutu a hannun sojojin Najeriya — Amnesty

Aƙalla fararen hula dubu 10 ne suka rasa ransu a hannun jami’an sojojin Najeriya, tun bayan fara yaƙin Boko Haram a shiyar Arewa maso Gabashin ƙasar. Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Amnesty International ce ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a kira yau Alhamis a Maiduguri, babban birnin Borno. ’Yan Majalisar Wakilai […]

Boko Haram: Fararen hula 10,000 sun mutu a hannun sojojin Najeriya — Amnesty

Aƙalla fararen hula dubu 10 ne suka rasa ransu a hannun jami’an sojojin Najeriya, tun bayan fara yaƙin Boko Haram a shiyar Arewa maso Gabashin ƙasar.

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Amnesty International ce ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a kira yau Alhamis a Maiduguri, babban birnin Borno.

Da yake jawabi, Shugaban Amnesty a Najeriya Malam Isa Sunusi, ya ce a lokuta da dama jami’an sojojin Najeriya na ɗaukar duk wani da ya fito daga yankin da mayaƙan Boko Haram suke, tamkar mamban ƙungiyar ta masu tada ƙayar baya ne.

“Sojojin Najeriya na ɗaukar duk wani wanda ke zaune ko kuma ya fito daga yankunan da Boko Haram su ke da iko da shi a matsayin mambar ƙungiyar.”

Malam Isa Sunusi ya ce sun shigar da ƙara gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da ke Hague, game da zargin cin zarafin ɗan adam da aka yi a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya ce muddin aka yi adalci ga rayukan da ba su ji ba su kuma gani ba da mayaƙan Boko Haram da kuma sojoji suka salwantar, to ba shakka nan ba da jimawa ba za a kawo ƙarshen yaƙin na Boko Haram.