Boko Haram: Fushin Allah ne a kan Najeriya – Mbadinuju
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Dokta Chinwoke Mbadinuju ya bayyana cewa Boko Haram wata azabtarwa ce daga Allah ga Najeriya saboda zaluncin da ake tafkawa a cikinta. Dokta Mbadinuju ya bayyana haka ne lokacin da yake bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, inda ya ce ta’addanci ba zai ragu ba sai kasar nan ta […]
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Dokta Chinwoke Mbadinuju ya bayyana cewa Boko Haram wata azabtarwa ce daga Allah ga Najeriya saboda zaluncin da ake tafkawa a cikinta.
Dokta Mbadinuju ya bayyana haka ne lokacin da yake bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, inda ya ce ta’addanci ba zai ragu ba sai kasar nan ta rungumi adalci.
“Ba za a kawar da ta’addanci ba, har sai an rugumi adalci a kasar nana. Abin da ya shafi mutanen Annabi Lud zai zama wasan yara idan ba a yi taka-tsantsan ba, kuma saboda wannan dalili ne yanzu mun san rashin adalci ke haifar da cin hanci da rashawa koma da za mu yi mata kwallaiya da wani suna.”
Tsohon Gwamnan ya ce ya bar PDP ne saboda rashin adalcin da ke cikinta. Game da komawarsa jam’iyyar adawa, ya ce: “Ya zama wajibi ya koma APC a yanzu, saboda shi ne abin da ya dace a yi. Domin a yayin da APC ta nuna cewa ita jam’iyya ce mai alkibla a yanzu da nan gaba, muna gani kiri-kiri duk wani abu mai kyau game da PDP yana bacewa. PDP ta zama azzalumar jam’iyya marar adalci da babu gaskiya a harshenta ba tausayi a zuciyarta ba amana a al’amuranta, abin da take yi kullum riya ne da yaudara.”
Ya ce, “Duk da cewa a matsayina na Gwamnan Anambra na yi bakin kokarin inganta rayuwar jama’ata a shekara hudu, amma adawar ’ya’yan jam’iyyar a jihar da hadin bakin fadar shugaban kasa ni kadai ne Gwamna mai ci da bisa zalunci PDP ta hana ni tikitin takara karo na biyu. Jam’iyyar ta nuna kamar ba ta yi min laifi ko ba ta yi wa dimbin al’ummar Anambara da na kyautata rayuwarsu a matsayina na gwamnansu ba. An yi watsi da mu da magoya bayanmu, kuma gwamnatin tarayya tana ci gaba da yin abu kamar babu wani dan Jam’iyyar PDP a Jihar Anambra.”
Ya kara da cewa: “Duk wanda gwamnati take hulda da shi in aka bincika sai a ga marar gaskiya ko marar basira inda hakan ya mayar marasa gaskiya da marasa basira suka zamo suke fada-aji a wurin gwamnati da siyasar kasar nan.”
Cif Mbadinuju ya ce ya yanke shawarar koma APC ne saboda burinsa na fitar da kasar nan daga ‘mugun halin’ da take ciki a yanzu. “Gaskiya bai kamata al’amura suka ci gaba da tafiya haka ba, a kyale al’umma su ruguje. Don haka nauyi ne a kan dukka masu tsoron Allah da masu karfin hali su mike tsaye su yi wani abu don fitar da kasar nana daga wannan mugun hali da take ciki.”
Ya ce yana mika cikakken goyon bayansa ga takarar Janar Muhammadu Buhari inda ya bukaci daukacin ’yan Najeriya su kada wa Jam’iyyar APC kuri’arsu a zaben na bana.