Boko Haram: Gidauniyar Daily Trust ta ba zawarawa tallafin Naira miliyan 10

Gidauniyar Daily Trust da Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya kafa ta ba da tallafin Naira miliyan 10 don horar da mata zawarawa 100 da suka rasa mazajensu a rikicin Boko Haram a Jihar Yobe.Da take bayani ga manema labarai a Damaturu game da tallafi, Kodinetan shirin Hajiya Halimatu Laminu […]

Boko Haram: Gidauniyar Daily Trust ta ba zawarawa tallafin Naira miliyan 10
Boko Haram: Gidauniyar Daily Trust ta ba zawarawa tallafin Naira miliyan 10

Gidauniyar Daily Trust da Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya kafa ta ba da tallafin Naira miliyan 10 don horar da mata zawarawa 100 da suka rasa mazajensu a rikicin Boko Haram a Jihar Yobe.
Da take bayani ga manema labarai a Damaturu game da tallafi, Kodinetan shirin Hajiya Halimatu Laminu Amshi ta ce shirin na horar da matan da suka rasa mazajensu sanadiyar rikicin Boko Haram an tsara shi ne da nufin samar musu da abin dogaro ta yadda za su tafi da harkokin yara marayun da ke gabansu cikin sauki.
Hajiya Halimatu Amshi ta ce kungiyarsu da ke kula da mata zawarawa da marayunsu ta kudiri aniyar amfani da tallafin da kamfanin na Daily Trust ya bayar na Naira miliyan 10 domin inganta rayuwar wadannan mata ’yan gudun hijira da ke jihar.
Hajiya Halima ta ce kungiyar ta zakulo mata hamsin-hamsin daga kananan hukumomin Fika da Damaturu don horar da su sana’o’in da suka hada da kiwon dabbobi da yin sabulu da man shafawa da dinki da matsar man gyada da makamantansu a matsayin wadanda za su fara cin gajiyar shirin.
Ta ce, kungiyar za ta tanadar wa matan kayayyakin da suka dace don fara koyon sana’o’in.
 Shugabar ta kuma ce a karkashin shirin tallafin na Gidauniyar Daily Trust, kungiyar za ta dauki dawainiyar yara marayu 50 don sa su a makarantun firamare daga kananan hukumomi biyu tare da samar da yunifom ga dalibai 100 don ba su karfin gwiwar yin karatu tare da horar da matan da ke shayarwa yadda za su shirya abincin mai gina jiki da za su ciyar da jiriransu.