Boko Haram: Gudunmawa jama’a!!!

A ’yan kwanakin nan matsalar yaki da Boko Haram ta kara kamari saboda kai hare-hare ga jami’an soja babu kakkautawa da ake yi wanda ya yi sanadiyyar rasuwar sojoji da dama. Al’amari na baya-bayan nan shi ne harin da ’yan Boko Haram suka kai wa sojoji a Metele ta Jihar Borno, inda suka yi shigar- burtu […]

Boko Haram: Gudunmawa jama’a!!!
Boko Haram: Gudunmawa jama’a!!!

A ’yan kwanakin nan matsalar yaki da Boko Haram ta kara kamari saboda kai hare-hare ga jami’an soja babu kakkautawa da ake yi wanda ya yi sanadiyyar rasuwar sojoji da dama.

Al’amari na baya-bayan nan shi ne harin da ’yan Boko Haram suka kai wa sojoji a Metele ta Jihar Borno, inda suka yi shigar- burtu suka kashe kwamandansu da sauran jami’an da yake tare da su a ofishinsa a lokacin.

Rahotonni sun nuna cewa ’yan Boko Haram din sun je sansanin sojan ne a cikin kayan soja, wanda ya sanya aka dauka abokan aiki ne, sai aka saki jiki da su har aka bar su suka shiga ofishin kwamandan sansanin, suna shiga sai aka rika jin karar bindigogi, ashe da shigarsu sun bude wuta ne suka kashe duk wadanda suka samu a ofishin kwanandan.

Wani rahoton kuma ya nuna cewa ’yan Boko Haram din suna da labarin cewa motocin yakin da aka girke a sansanin mushen gizaka ne kin mutu kina ba yara tsoro, domin an ce motocin yakin tsofaffi ne da aka sayo su tun zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Alhaji Shehu Shagari. Saboda haka suka fada wa sojojin da ke sansanin da harbi babu kakkautawa saboda suna da labarin karfin makamansu, wannan shigar saurin da suka yi wa sojoji ya sanya an yi asarar sojoji masu yawa a wannan harin da aka kai.

Sannan kuma a yayin da aka tura wadansu sojojin domin su kwaso gawarwakin ’yan uwansu da aka kashe sai ’yan Boko Haram din suka sake fado musu suka karkashe wadansu.

Kamar yadda dan Majalisar Wakilai Gudaji Kazaure ya bayyana, ya ce lallai akwai alamun cewa babu kyakkyawar alaka tsakanin sojan sama da sojan kasa, domin kamar yadda ya bayyana, ’yan Boko Haram din sun kwashe sa’o’i masu yawa suna artabu da sojojin sansanin ba tare da samun dauki daga sojan sama ba, saboda wai ba su samu umarni daga hedkwatarsu da ke Abuja ba. Wannan ya sanya ake zargin cewa akwai rashin jituwa a tsakanin sojan kasa da sojan sama, idan hakan ya kasance gaskiya al’amari ya lalace ke nan.

Domin haka daga abin da ya faru a sansanin soja na Metele za a fahimci cewa akwai masu ba ’yan Boko Haram labari daga cikin sojoji, wanda hakan ya sanya suka san sirrinsu. Wannan ya sanya rayuwar sojojin a cikin hadari domin babu yarda a tsakaninsu.

Akwai kuma zargin da ake yi cewa ana karkatar da kudin da aka ware domin sayen makamai, idan har ya kasance ba a ba sojoji makaman da suka dace, to lallai ba a kyauta ba kuma ba a yi dabara ba, domin idan al’amarin ya gagare su har ya kasance ’yan Boko Haram suka yi galaba, to babu wanda zai sha, saboda ko mutum ya tara dimbin dukiya ba zai sanya ya tsira ba, don haka gara ya taimaka a samu nasara ko da zai zauna babu ko kwabo, ya fi ya tara dukiyar da zai rasa inda zai zauna ya ci.

Irin wannan hali na rashin yarda ne ya kara haifar da matsalar yaki da ta’addanci a Jihar Zamfara inda kwanan nan aka kori wadansu sarakuna daga aiki saboda ana zarginsu da taimaka wa ’yan ta’adda.

To jama’a, a irin wannan hali ta yaya za a kai ga nasarar yaki da ta’addanci, alhali ana tare da munafukai? Saboda haka lallai ne kowa da kowa ya tashi ya bayar da gudunmawa domin magance wannan matsalar. Ya kamata a taimaka wa sojojin nan da addu’a dare da rana domin su kawo karshen wannan matsala da ta addabe mu.

Haka kuma ya kamata a daina sanya harkar siyasa a batun tsaro, da gwamnati da ’yan adawa duk ya kamata ne a taru a gano hanyar magance wannan matsalar, kada ’yan adawa su dauka matsala ce ta gwamnati kawai.

Su ma kafofin watsa labarai ya kamata su kara kula, domin ba kowane labari ne ya dace su rika yadawa ba saboda yin hakan yana kara firgita jama’a kuma yana raunana sojojinmu, wani labarin ko gaskiya ne bai kamata a yada shi ba, balle kuma mafi yawan irin wadannan labaran masu tayar da hankali a kan ce wai an samo su ne daga wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta.

Haka kuma kafofin sada zumunta suna taimakawa sosai wajen yada labaran karya kuma hakan yana yin matukar illa game da yakin da ake yi da Boko Haram, domin ana yada farfaganda sosai ta wannan hanyar.

A sakamakon bullowar kafofin sada zumunta a yau an wayi gari kowa ya zama dan jarida, shi ya sanya ake yada labarai marasa tushe saboda babu ka’ida, sai mutum ya kirkiri labarin karya ya watsa kuma mutane su yarda. Misali, akwai wani lokaci a baya da wata yarinya ta rubuta cewa idan an sha ruwan gishiri kuma aka yi wanka da shi da tsakar dare kafin gari ya waye za a tsira daga cutar Ibola da ta kunno kai a lokacin, da ta watsa a kafar sada zumunta mutane da dama sun yarda kuma nan da nan labarin ya watsu kamar wutar daji, kowa yana kokarin ya yi wanka da ruwan gishiri kafin gari ya waje, alhali labarin kirkirarsa aka yi.

Saboda haka ya kamata mutane su rika kokarin tantance duk labarin da suka gani a kafar sada zumunta kafin su yada shi, domin mafi yawan labaran kirkiransu aka yi.

Su kuma jami’an soji ya kamata su hada kansu domin ta haka ne kawai za su kai ga nasara a wannan yaki da suke da Boko Haram.

Jama’ar kasa kuma akwai bukatar su karfafa wa sojoji gwiwa, su rika yi musu addu’ar samun nasara a kowane lokaci, domin saboda su ne suka sadaukar da rayukansu.

Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen wannan fitina, Ya kuma tausasa zukatan masu ta’addancin nan da suke kashe mutane babu tausayin mata da yara da tsofaffi.