Boko Haram: Gwamna Kashim Shetima ya jinjina wa jami’an tsaro
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shetima ya jinjina wa jami’an tsaron Najeriya da Kamaru da Chadi kan kokarinsu na fatattakar mayakan Boko Haram masu tayar da kayar baya. Gwamna Kashim Shetima, ya yi jinjinar ce lokacin da ya ziyarci Gombe a ci gaba da yakin neman zabensa a Kudancin Borno da ke makwabtaka da Jihar […]
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shetima ya jinjina wa jami’an tsaron Najeriya da Kamaru da Chadi kan kokarinsu na fatattakar mayakan Boko Haram masu tayar da kayar baya.
Gwamna Kashim Shetima, ya yi jinjinar ce lokacin da ya ziyarci Gombe a ci gaba da yakin neman zabensa a Kudancin Borno da ke makwabtaka da Jihar Gombe, inda ya ce yanzu ana samun nasara sosai a kan mayakan Boko Haram. Ya ce ‘yan Boko Haram din wadanda suka san sassan jihar kuma suke shiga suna kashe mutane yanzu da aka fatattake su daga Maiduguri ne suka dawo Kudunci Borno, hakan a cewarsa ya sa yanayin tsaro a garuruwan Chibok da Damboa da Gwoza da Hawul ya zama abu wani daban. Gwamna Shetima, ya ce duk da haka yanzu an yi nasarar korarsu daga garuruwan Baga da Damasak da Marte da Gamborun Ngala, shi ya sa suke shigowa ta wasu hanyoyi suna shiga ta dajin Sambisa zuwa Kudancin Borno. Ya ce Jihar Borno ta ninka Jihar Legas sau 20 a fadin kasa ta ninka Jihar Abiya sau 14, kuma idan aka hada jihohin Kudu maso Kudu gaba dayansu Borno ta yi ukunsu a girman kasa, ya ce kasancewar ‘yan Boko Haram din ‘ya’yan yankin ne ya sa suka san lungu da sakon da suke shiga har su kai hare-hare a wurare daban-daban. Alhaji Kashim Shetima, ya ce sai dai wani abin damuwa shi ne akwai wasu ‘yan tsiraru musamman da suke kokarin a dage zabe don ganin ba za su ci zaben ba.