Boko Haram: Jihar Sakkwato ta kai tallafi ga jama’ar Yobe
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kai tallafin kayayyaki ga al’ummar da suke fuskantar matsalar rayuwa sakamakon rikicin Boko Haram da ya kai su ga barin yankunansu a Jihar Yobe. Da take mika kayayyakin tallafin ga gwamnatin jihar ta Yobe jagorar tawagar gwamnatin Jihar Sakkwato, Kwamishinar Ma’aikatar Harkokin Mata Hajiya Kulu Abubakar, ta ce sun kai kayayyakin […]
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kai tallafin kayayyaki ga al’ummar da suke fuskantar matsalar rayuwa sakamakon rikicin Boko Haram da ya kai su ga barin yankunansu a Jihar Yobe.
Da take mika kayayyakin tallafin ga gwamnatin jihar ta Yobe jagorar tawagar gwamnatin Jihar Sakkwato, Kwamishinar Ma’aikatar Harkokin Mata Hajiya Kulu Abubakar, ta ce sun kai kayayyakin tallafin ne don taimaka wa al’ummar da wannan bala’i ya shafa da zimmar samun kyautatuwar rayuwa tare da kara inganta dangantakar da ke tsakanin Jihar Sakkwato da kuma Jihar Yobe.
Jagorar tawagar ta kara da cewa kayayyakin tallafin da suka kai sun hada da buhunan shinkafa 1,200 da turamen atamfa 1,000 da sauransu.
Da yake karbar kayayyakin tallafin a madadin gwamnatin Jihar Yobe, Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barista Ahmed Mustafa Goniri ya nuna matukar jin dadin gwamnatin jihar dangane da kayayyakin tallafin da gwamnatin Jihar Sakkwato ta kai wa al’ummar jihar da suka fuskanci rikicin Boko Haram.
Ya ba da tabbacin cewa wadannan kayayyakin tallafi za a ba da su ga al’ummar da lamarin ya shafa cikin adalci.
Tawagar ta Jihar Sakkwato ta kai ziyarar gani da ido ga wani sashi na al’ummar da bala’in ya shafa da ke wani sansani a makarantar firamare ta Pomfamari a cikin garin Damaturu domin jajanta musu.