Boko Haram: Jonathan da Nyako sun fara asakala

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zargi gwamnonin jihohin yankin Arewa-maso-Gabas, inda ya bayyana cewa sakacinsu ne ya jawo rikicin Boko Haram a yankin.Shugaban ya ce gwamnonin Jihohin Adamawa da Barno da kuma Yobe su ne suka fi kowa alhaki sakamakon sakacinsu, wanda shi ne ya haifar da yanayin da ya sa ’yan kungiyar Boko Haram […]

Boko Haram: Jonathan da Nyako sun fara asakala

Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zargi gwamnonin jihohin yankin Arewa-maso-Gabas, inda ya bayyana cewa sakacinsu ne ya jawo rikicin Boko Haram a yankin.
Shugaban ya ce gwamnonin Jihohin Adamawa da Barno da kuma Yobe su ne suka fi kowa alhaki sakamakon sakacinsu, wanda shi ne ya haifar da yanayin da ya sa ’yan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da cin karensu ba babbaka a yankin.
Ya bayyana hakan ne a wani taron jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa-maso-Gabas da aka yi a Jihar Bauchi ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce abin kunya ne gwamnonin su dangana tabarbarewar tsaron yankin nasu da Gwamnatin Tarayya.
“Wannan abin kunya ne ga gwamnan da ya shafe fiye da shekaru shida yana mulkin jiharsa ya tunkaro ni da batun cewa rashin kyakkyawan shugabancin ne ya jawo wannan matsalar tsaron, bayan fiye da rabin matasan da suke jiharsa ko shaidar karatun firamare ba su da ita kuma ya kasa yin komai game da hakan.” Inji Shugaba Jonathan
Ya ci gaba da cewa, “A gaskiya ya dace gwamnonin jihohi su ji kunya, idan suka ce rashin bai wa matasa karatun firamare da na  sakandare ne ya sa su shiga harkarkokin tada zaune tsaye a yankunansu.
Shugaban ya ce ba zai manta ba, “A lokacin da nake mataimakin gwamnan Jihar Bayelsa da ma lokacin da nake gwamnan jihar mun yi fama da matsalolin tsaro kuma cikin wani lokaci muka shawo kansu. Alhakin tura yara makarantun firamare da sakandare ba ya rataya ne a wuyan Gwamnatin Tarayya ba, tsarin mulkin Najeriya ya dora wa Gwamnatin Tarayya alhakin samar da ilimin gaba-da-sakandare ne kuma mun samar da shi”.
Shugaban ya ci gaba da cewa, “Ya za ka bar matasa cikin yunwa, su je su yi ta kashe matane? Jihar Bayelsa ce ta farko-farko da aka fara fuskantar matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa kuma muka yi maganin matsalar a wancan lokacin.”
Daga bisani ya bayyana cewa matsalar tsaron da abin takaici ne, tare da yin alwashin cewa gwamnatinsa za ta dauki matakan da duk suka dace don ganin bayan matsalar tsaron.
“Halin da ake ciki a yankin Arewa-maso-Gabas abin bakin ciki ne, amma a matsayinmu na hukuma muna yin iyakar kokarinmu don tabbatar da cewa zaman lafiya ya komo yankin, ta yadda ci gaban da aka san yankin da shi a baya zai dawo.” Inji shi.
Ya bayyana cewa wannan kalubalen tsaron na dan wani lokaci ne. Shugaban ya kuma yi alkawarin kawar da fatara da kuma samar da abubuwan more rayuwa a yankin na Arewa-maso-Gabas.
A karshe dai ya ce za a samar da tsaro a duk fadin kasar nan, saboda kowane dan Najeriya ya samu ’yancinsa na walwala ba tare da tsoro ba. “Rikicin Boko Haram a Arewa-maso-Gabas, ga satar mutane don neman kudin fansa a yankin Kudu-maso-Kudu, sai kuma matsalar ’yan fashi-da-makami a yankin Kudu-maso-Gabas. Wadannan duk matsalolin tsaron ne kuma ya zama wajibi mu kawo karshensu.” Inji shi.
Sai dai da yake mayar da martani ga shugaban kasan ta bakin Daraktan Yada Labaransa, Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya ce ya yi mamakin yadda Shugaba Jonathan yake kara dora alhakin kasawar shugabancinsa ga kowa da kowa. A cewarsa, zargin da yake wa gwamnonin na yin sakaci bai dace ba, saboda hakan ba alama ce ta iya shugabanci ba.
Ya ce, yana so ya yi amfani da wannan damar don ya ja hankalin shugaban kasa game da sama da ajujuwa 800 da aka lalata sakamakon rikicin Boko Haram a Jihar Barno da kuma wadansu fiye da 2,000 a Jihar Yobe. A kwanakin baya ma a Jihar Adamawa an lalata wadansu ajujuwan.
Ya ci gaba da cewa, “An lalata wasu makarantun kuma an rufe wadansu, ciki har da wadansu da suke mallakin Gwamnatin Tarayya ne, duk da cewa shugaban kasa ya ce ba aikin Gwamnatin Tarayya ba ne samar da ilimin sakandare.
“Sai kuma batun rashin ziyartarsa jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa, wanda za a iya fassara hakan da kasa sauke nauyin da tsarin mulki ya dora masa na kare lafiya da rayukan kowane dan Najeriya. Idan harkokin siyasa za su kai shi Jihar Bauchi, me zai hana ya ziyarci Jihohin Barno da Yobe?” Inji shi.
Gwamnan ya ce, idan akwai wata alama ta rashin kyakkyawan shugabanci, to tana tattare da yadda shugaban kasa yake gudanar da ayyukansa da kuma irin kalaman da ke fitowa daga bakunan masu magana da yawunsa.
Ya ce gwamnoni ba su da laifi ko kadan ta bangaren tabarbarewar tsaro a yankin Arewa-maso-Gabas, saboda alhakin tsaron kasa ya rataya ne kacokan a wuyan Gwamnatin Tarayya. “Shugaban kasa ne Kwamandan Askarawan kasar nan kuma shi ne ikon sarrafa dukkanin dakarun kasar nan ke hannunsa, ciki har da rundunar ’yan sanda da hukumar kwastam da duk wadansu jami’an tsaro na kasar nan. Idan kuma aka komo batun ilimi, shugaban kasa ya saki hanya ko kuma in ce yana cikin duhun kai”. Inji shi.
Gwamnan ya kuma kalubalanci Shugaba Jonathan da ya fadi wani aikin ci gaba da ya taba yi wa Jihar Adamawa tun bayan darewarsa shugabancin kasar nan.
Shi ma a nasa martanin, Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima ya ce ba ya so ta kai su da yin sa-in-sa da shugaban kasa. Shi ya sa ba zai ce komai ba  kan batun.
Mai ba gwamnan shawara kan Harkokin Yada Labarai, Malam Isa Gusau ya bayyana cewa kila ba haka shugaban kasa yake nufi ba. Amma Shugaba Jonathan ya kwana da sannin tushen rikicin da yankin ke fama da shi.
Ya kara da cewa, “Idan ka zanta da Ministan Ayyukan Musamman Kabiru Tanimu Turaki, wanda shi ke jagorantar tattaunawar sulhu da ’yan kungiyar Boko Haram, za ka ji ya ce akwai masu rike takardun digiri mai daraja ta daya a cikin mambobin kungiyar. Ka ga akwai ’yan kungiyar ta Boko Haram da suke da karatu ke nan. Kuma mukan ji an ce akwai wadansu daga cikin ’yan kungiyar da suka yi watsi da karatunsu don su shiga kungiyar ta Boko Haram, sannan akwai wadansu kuma da suka yayyaga takardun shaidar kammala karatunsu”.
A karshe, ya ce matsalar ba ta ta’allaka ba ne da rashin ilimi kawai. “Mun yi amannar cewa shugaban kasa ya san inda gizo ke sakar, shi ya sa muke ganin kila ba haka yake nufi ba”. Inji shi.