Boko Haram: Kannywood ta tallafa wa ’yan gudun hijira a Kano

A ranar Juma’ar makon jiya masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa da suka hada da jarumai da ’yan kasuwa da daraktoci da furodusoshi suka ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, wadanda aka tsugunnar a ofishin Hisba na Kano, inda suka tallafa musu da kayayyakin jinkai.Alhaji Isma’il […]

Boko Haram: Kannywood ta tallafa wa ’yan gudun hijira a Kano
Boko Haram: Kannywood ta tallafa wa ’yan gudun hijira a Kano

A ranar Juma’ar makon jiya masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan Hausa da suka hada da jarumai da ’yan kasuwa da daraktoci da furodusoshi suka ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, wadanda aka tsugunnar a ofishin Hisba na Kano, inda suka tallafa musu da kayayyakin jinkai.
Alhaji Isma’il NaAbba Afakallah ne ya jagoranci ’yan fim din don kai gudunmuwarsu ga wadanda rikicin Boko Haram din ya shafa.
Ya ce idan aka duba za a ga yadda kungiyoyi da jama’a suke bada gudunmuwarsu ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, don haka Kannywood ba za ta yi kasa a gwiwa wajen bayar da gudunmuwarta ba.
Ya ce: “Mun ziyarci ’yan gudun hijirar da suke ofishin Hisbah a Kano don jajanta musu. ’Yan gudun hijirar da muka gani sun fi mutum dubu biyu, inda aka rarraba su zuwa gidaje daban-daban, don haka kungiyar Kannywood ta kai musu gudunmuwar kayayyaki a karkashin jagorancina.”
Ya ce Kannywood ta kai musu buhun shinkafa 8 da buhun siga da ganyen shayin katan daya da lita 50 ta man gyada da tufafi na mata da katan din Indomie biyar da sauran kayayyaki.
Ya ce abubuwan da suka gani dole mutum ya zubar da hawaye, don haka ya bukaci jama’a su taimaka wa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa domin suna cikin mawuyacin hali.
“Abin da muka gani ya daga mana hankali, hakan ya sanya muka tattauna yadda za mu sake hada wadansu kayayyaki mu kara kai musu.” Inji shi.
A cikin ’yan fim din suka yi wa Afakallah rakiya akwai Misbahu M Ahmad da Salisu Mohammed Ofisa da Tahir Fagge da Tijjani Asase da Sadik M. Mafia da sauransu.