Boko Haram: kasashen Tafkin Chadi sun gana a Abuja
Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi da kuma Jamhuriyar Benin, sun gana jiya Alhamis a Abuja, birnin tarayyar Najeriya, a wani yunkurin daukar muhimman matakai na kafa rundunar hadin gwiwar da za ta yaki kungiyar Boko Haram. Shugaban Najeriya, Muham-madu Buhari ya ce kasarsa ce ya kamata ta rike shugabancin rundunar hadin-gwiwa da […]
Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi da kuma Jamhuriyar Benin, sun gana jiya Alhamis a Abuja, birnin tarayyar Najeriya, a wani yunkurin daukar muhimman matakai na kafa rundunar hadin gwiwar da za ta yaki kungiyar Boko Haram.
Shugaban Najeriya, Muham-madu Buhari ya ce kasarsa ce ya kamata ta rike shugabancin rundunar hadin-gwiwa da za a kafa domin yaki da kungiyar.
A jawabinsa lokacin taron da sauran shugabannin kasashen wato, Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da kuma Benin, Shugaba Buhari ya ki amincewa da bukatar a dinga karba-karba na shugabancin rundunar tsakanin Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar da kuma Benin.
kasashen da suka halarci taron dai sun hada da Najeriya da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Nijar da kuma Benin.
Taron dai na zuwa ne bayan tarukan da manyan hafsoshin sojin kasashen suka yi ranar Talata da wanda ministocin tsaronsu suka yi shekaranjiya Laraba, inda suka shata wasu manufofi na tabbatar da nasarar yaki da ta’addanci.
Har ila yau, shugabannin suka umarci Hukumar Raya Tafkin Chadi da ta bullo da wani shiri na samar wa matasa ayyukan yi da nufin taimakawa wajen rage talauci a yankin Arewa- maso-Gabashin Najeriya da kuma sauran yankunan da tashe-tashen hankula na mayakan kungiyar Boko Haram suka lalata.