Boko Haram: Ma’aikatan Bankin FMB daga Arewa maso Gabas sun kai tallafi

Ma’aikatan Bankin Bada Rancen Gina Gidaje na kasa (FMB) ’yan asalin jihohin Arewa maso Gabas da ke fama da masu tada kayar baya sun bayar da tallafin kayan abinci ga wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu da ke zaman gudun hijira a makarantar firamare ta Unguwar Fomfari a garin Damaturu a Jihar Yobe. […]

Boko Haram: Ma’aikatan Bankin FMB daga Arewa maso Gabas sun kai tallafi
Boko Haram: Ma’aikatan Bankin FMB daga Arewa maso Gabas sun kai tallafi

Ma’aikatan Bankin Bada Rancen Gina Gidaje na kasa (FMB) ’yan asalin jihohin Arewa maso Gabas da ke fama da masu tada kayar baya sun bayar da tallafin kayan abinci ga wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu da ke zaman gudun hijira a makarantar firamare ta Unguwar Fomfari a garin Damaturu a Jihar Yobe.

Da ya ke bada kayan tallafin Manajan Bankin FMB na Damaturu Alhaji Abdu Goni ya ce sun kawo tallafin ne domin rage wahalhalun rayuwa ne ga jama’ar da wannan rikici ya fada musu, ya kai ga raba su da yankunansu na asali.
Manajan ya kara da cewa, su ma’aikatan bankin FMB, da suka fito daga jihohin Arewa maso Gabas sun yi wannan yunkuri ne a matsayin hanyar da za su iya bi baya ga addu’a don taimakawa wa wadanda hare-hare suka raba su da muhallansu.
Ya kara da cewa sun himmatu wajen bayar da kayan tallafin ne ga’yan gudun hijirar ne a jihohin Yobe da Borno da Adamawa da kuma Birnin Tarayya, Abuja.
Da yake jawabi a madadin ’yan gudun hijirar, Malam Bulama Modu godiya ya yi ga ma’aikatan bankin na FMB kan damuwar da suka nuna game kan halin da suke ciki har suka kawo musu dauki.