Boko Haram: Majalisar dinkin Duniya ta bukaci a kafa rundunar sojin Afirka

Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya bukaci kasashen Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya su gaggauta kafa runduna mai karfi da za ta murkushe kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da zama barazana ga yankin. Majalisar dinkin Duniyar ta kuma yi Allah wadai da ayyukan Boko Haram kan yadda take ci gaba […]

Boko Haram: Majalisar dinkin Duniya ta bukaci a kafa rundunar sojin Afirka
Boko Haram: Majalisar dinkin Duniya ta bukaci a kafa rundunar sojin Afirka

Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya bukaci kasashen Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya su gaggauta kafa runduna mai karfi da za ta murkushe kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da zama barazana ga yankin. Majalisar dinkin Duniyar ta kuma yi Allah wadai da ayyukan Boko Haram kan yadda take ci gaba da amfani da kananan yara a matsayin ’yan kunar bakin wake tare da yin garkuwa da mata da yara.

Majalisar ta bukaci kasashen da ke makwabtaka da Najeriya su kafa rundunar hadin gwiwa domin aikin yaki da Boko Haram kamar yadda suka amince tun bara.
Kwamitin Sulhun ya kuma bukaci kasashen su amince da tsarin musayar bayanan tsaro na sirri a tsakaninsu domin kawo karshen barazanar Boko Haram a yankin.
A wani labarin kuma kungiyar Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo, inda ta ce ita ke da alhakin mummunan harin da aka kai garin Baga da ke Jihar Borno mako biyu da suka gabata.
A cikin bidiyon, shugaban kungiyar Abubakar Shekau, ya yi barazanar cewa kungiyar za ta zafafa hare-hare a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Bidiyon, mai tsawon minti 35, ya nuna Abubakar Shekau yana nuna tarin makaman sojojin Najeriya da kungiyar ta samu bayan harin na Baga.
Shekau ya ce za su kai hari a Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar.
kungiyar ta fitar da bidiyon ne a daidai lokacin da Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar ke gudanar da babban taro a Yamai domin nemo hanyoyin yaki da ita.
A ranar Asabar, kasar Chadi ta tura dakarunta da motocin soji 400 zuwa Kamaru domin taimakawa wajen yaki da kungiyar.