Boko Haram: Mata ’yan gudun hijira 410 za su haihu a watan gobe
Ana sa ran mata ’yan gudun hijirar Boko Haram 410 ne za su haihu a watan gobe a sansanonin ’yan gudun hijira daban-daban da ke Maiduguri a Jihar Borno. Masu juna biyun an zakulo su ne daga cikin mata 1,980 da aka gano suna da ciki a sansanonin ’yan gudun hijira 13 da aka kebe […]
Ana sa ran mata ’yan gudun hijirar Boko Haram 410 ne za su haihu a watan gobe a sansanonin ’yan gudun hijira daban-daban da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Masu juna biyun an zakulo su ne daga cikin mata 1,980 da aka gano suna da ciki a sansanonin ’yan gudun hijira 13 da aka kebe wa mata daga cikin sansanoni 23 da ake da su a garin Maiduguri.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta tabbatar da cewa akwai mata 410 masu juna biyu a sansanonin wadanda ake sa ran za su iya haihuwa a kowane lokaci na watan gobe wato Satumba.
Hukumar NEMA ta ce a halin yanzu ta riga ta yi duk wani shiri na samar da kwararrun ungozoma da kayan aiki isassu da akwatunan taimakon haihuwa domin ta tabbatar masu junan sun sauka lafiya kuma jariran da suka haifa sun samu kulawar da suke bukata a kan lokaci.
A halin yanzu an riga an ba duk wata mai juna akwatin kayan haihuwa da ya kunshi kayan jarirai kamar su zane da kwalabar ba da abincin jirirai da shimfidar jarirai da abin shimfida da kuma gidan sauro na jariran kamar yadda hukumat ta bayyana, kuma ta ce an hada musu da jakar kayan raino da kwando da tawul da kunzugun zamani (famfas) da madara da milo domin masu shayarwar.
A wani taro da aka yi a Maiduguri, an rawaito cewa Shugaban Hukumar NEMA ta kasa Muhammad Sani Sidi yana cewa a tarihin Najeriya Jihar Borno ce ta fi kowace jiha samun matsalar ’yan gudun hijira inda hakan ya janyo aka samar da sansanin ’yan gudun hijira 23 a jihar.
Sani Sidi ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince a kara samar da sansanonin ’yan gudun hijira guda biyu da za su tsugunar da mutum dubu 12, domin ’yan gudun hijirar da aka koro su daga Kamaru.
“Kashi 60 cikin 100 na mazauna sansanonin ’yan gudun hijira mata ne da yara kanana wadanda aka sa su a cikin wadanda rayuwarsu ke cikin barazana kuma suke bukatar taimako na musamman a cikin gaggawa. A dalilin haka ne aka ware mata masu juna biyu 410 daga cikin 1,980 wadanda aka gano suna da juna a sansanonin ’yan gudun hijira na mata 13 a Maiduguri,” inji Sani Sadi a wata takarda da Kakakin Hukumar Malam Sani Datti ya rattaba wa hannu.