Boko Haram matsala ce ta kasa ba Arewa kadai ba – Sule Lamido

Hare-haren ta’addanci da suka addabi yankin Arewa maso Gabas, matsala ce ta kasa baki daya ba yankin Arewa kawai ba, kuma akwai bukatar gudunmawar kasar don kawar da ita. Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ne ya bayyana haka a wurin wata muhawara da Cibiyar Kukah da ke shirya a kan al’amuran kasa a Abuja. […]

Boko Haram matsala ce ta kasa ba Arewa kadai ba – Sule Lamido
Boko Haram matsala ce ta kasa ba Arewa kadai ba – Sule Lamido

Hare-haren ta’addanci da suka addabi yankin Arewa maso Gabas, matsala ce ta kasa baki daya ba yankin Arewa kawai ba, kuma akwai bukatar gudunmawar kasar don kawar da ita.
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ne ya bayyana haka a wurin wata muhawara da Cibiyar Kukah da ke shirya a kan al’amuran kasa a Abuja. Gwamnan ya ce matsalar Boko Haram a Arewa da fasa bututun mai a yankin Neja Delta da garkuwa da jama’a a Kudu maso Gabas, matsaloli ne na kasa kuma ba daidai ba ne a rika dora alhakin magance al’amarin a kan gwamnatoci da jagororin Arewa kadai.
Abokin muhawaransa, Gwamnan Jihar Legas Babatunde Fashola cewa ya yi alhakin kuvutar da ’yan matan Chibok ya rataya ne a kan mutum guda, kuma shi ne Shugaban kasa wanda shi ne Babban Kwamandan Askarawan kasa. Gwamnonin biyu sun bayyana haka ne a karshen muhawarar a lokacin yin tambayoyi daga mahalarta taron. Wata ’yar kungiyar fafutukar ’yantar da ’yan matan Chibok ta kalubalanci Gwamna Lamido don jin abin da shi da gwamnonin Arewa ke yi game da halin da yankin ke ciki.
Tun farko a jawabin Shugaban Cibiyar, Bishop Hassan Matthew Kukah, ya ce burin cibiyar shi ne samar da mafita a kan al’amura da suka addabi kasa ta hanyar shirya muhawara a tsakanin vangarori mabanbanta, cikin girmama ra’ayi da martaba al’adun juna.