Boko Haram: Mutanen Borno sun soma azumi da addu’o’i

Ranar Litinin mutanen jihar Borno sun tashi da azumi da addu’o’i da don neman saukin mayakan kungiyar Boko Haram da suka jefa su a ciki. Fiye da shekara 10 ‘yan Boko Haram na kai hare-hare musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa. A makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Borno Umara Zulum, […]

Boko Haram: Mutanen Borno sun soma azumi da addu’o’i

Wasu daga cikin malaman suke addu’o’i a masallaci

Ranar Litinin mutanen jihar Borno sun tashi da azumi da addu’o’i da don neman saukin mayakan kungiyar Boko Haram da suka jefa su a ciki.

Fiye da shekara 10 ‘yan Boko Haram na kai hare-hare musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

A makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Borno Umara Zulum, ya bukaci al’ummar jihar da su yi azumi ranar Litinin.

Gwamna Zulum, ya kara da cewa Shehun Borno ya tabbatar masa da cewa duka limamai na kananan hukumomi 27 da ke jihar za su yi addu’o’i da Qunuti a duka salloli biyar na ranar Litinin.

 

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa