Boko Haram na barazanar sake kashe jami’in kiwon lafiya a Borno

Mayakan Boko Haram  na barazanar sake kashe daya daga cikin biyu na jami’an kiwon lafiya da suka yi garkuwa da su a garin Rann dake jihar Borno fakon wannan shekarar. Tun a watan Satumba ‘yan kungiyar suka kashe Saifura Hussaini Khorsa, yayin da suke gargadin zasu kashe Hauwa Mohammed Liman da Alice Loksha. A wata […]

Boko Haram na barazanar sake kashe jami’in kiwon lafiya a Borno
Boko Haram na barazanar sake kashe jami’in kiwon lafiya a Borno

Mayakan Boko Haram  na barazanar sake kashe daya daga cikin biyu na jami’an kiwon lafiya da suka yi garkuwa da su a garin Rann dake jihar Borno fakon wannan shekarar.

Tun a watan Satumba ‘yan kungiyar suka kashe Saifura Hussaini Khorsa, yayin da suke gargadin zasu kashe Hauwa Mohammed Liman da Alice Loksha.

A wata sanarwa da kwamitin kungiyar Red ta duniya (ICRC) ta fitar wanda majiyarmu ta samu rahoton cewa, ‘yan kungiyar zasu kashe Liman jami’ar kiwon lafiyan idan ba  a sasanta ba a cikin sa’o’i 24.