Boko Haram na iko da yankin da ya fi jihohi uku girma – Bincike
Yanzu haka mayakan Boko Haram sun kwace yanki mai girman murabba’in kilomita dubu 20 a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke Arewa maso Gabas, kamar yadda binciken Aminiya ya gano. Yankin ya fi jihohin Imo da Abiya da Ekiti girma idan aka hada su, kuma ya kai girman Jihar Bayelsa yayin da ya […]
Yanzu haka mayakan Boko Haram sun kwace yanki mai girman murabba’in kilomita dubu 20 a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke Arewa maso Gabas, kamar yadda binciken Aminiya ya gano.
Yankin ya fi jihohin Imo da Abiya da Ekiti girma idan aka hada su, kuma ya kai girman Jihar Bayelsa yayin da ya dara girman Jihar Gombe.
Fadin kasar da mayakan ke iko da shi ya kai kusan girman yankin Wales da ke kasar Ingila ko Jihar Marylandb da ke Amurka, kuma ya fi Arewacin Ireland.
Yankin yana dauke da sama da mutum miliyan biyu, kuma ya hada da kananan hukumonmi 10 da suka hada da Bama da Dikwa da Ngala da Kala-Balge da Gwoza a Jihar Borno; sai Madagali da Michika da Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa da kuma Gujba da Gulani a Jihar Adamawa, kuma jimillar yankin da suka kwace ya kai murabba’in kilomita dubu 21 da 545 da digo 86.
Tuni shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ayyana yankin da suka kwace da bangare na Daular Musulunci mai hedkwata a garin Gwoza.
Sai dai ana jin Shekau yana zaune na dajin Sambisa inda daga can ne yake aiwatar da fasalin dokokin Musuluncin da yake da’awa a yankunan da mayakansa suka kame.
Dubban jama’a ne suka kaurace daga yankunan da aka kwace inda suka gudun hijira a matsugunnai daban-daban a jihohin uku da sauran sassan kasar nan, yayin da wasu dubban suka tsallaka zuwa Jamhuriyyar Nijar da Kamaru.
Akwai dimbin mutane da suke ci gaba da zama bayan an ritsa su, ciki har da mata da kananan yara da ake kashe su ta hanyar dauki dai-dai.
Farkon bayyanar mayakan kungiyar sun rika kashe shugabannin al’umma da jami’an gwamnati, sannan suka fada kan malamai da shugabannin addini da matasan da suke kawo musu cikas.
Wani mutum da ya gudo daga Bama bayan mayakan Boko Haram sun kwace garin a watan Satumba ya ce, “Rayuwa a kasar Boko Haram akwai tsanani. Sukan kashe ko su musguna tare da cutar da jama’a ba tare da wani dalili ba. Sun tafi da mata masu kananan shekaru da ’yan mata; kuma suna kwashe dukiyar da mutane suka gudu suka bari a matsayin ganimar yaki.”
A lokacin da Shugaba Jonathan ya je taron Majalisar dinkin Duniya a birnin New York na Amurka ya ce kimanin mutum dubu 13 ne aka kashe tun barkewar rikicin Boko Haram a shekarar 2009. Sai dai hukumomin soja sun ki cewa uffan kan adadin sojojin da aka kashe a kokarin kwantar da wutar rikicin.
Rikicin ya kazanta inda ya shafi kowane bangare na rayuwa a yankin. An lalata dukiya ta biliyoyin Naira a Arewa maso Gabas, musamman a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.
dalibai da dama ba su zuwa makaranta a sassa da daman a jihohin uku da mayakan ke da karfi. A Jihar Borno kwanakin nan ne gwamnati ta bayar da sanarwar za a bude makarantu bayan shafe wata bakwai a rufe.
Mayakan sun fara fadada daularsu ce tun farkon damina, kuma a yanzu haka gonaki da dama sun lalata sakamakon gudun ceton rai daga yankunan da lamarin ya shafa.
Da suke tofa albarkacin bakinsu kan yaki da sojoji ke yi da maharan, wasu manyan jami’an soja da suka yi ritaya sun shaida wa Aminiya cewa, wajibi ne gwamnati da manyan jami’an sojojin kasar nan su nuna karin sadaukar da kai fiye da yadda suke yi a yanzu.
“Wajibi ne Shugaban kasa ya nuna gaskiya kan yadda yake fuskantar yakin. kasar nan ta rasa yankunanta; ana kashe sojoji tare da asarar makamai ga mahara. Wannan ba alheri ba ne ga gwamnati da kasar,’ inji wani Kanar mai ritaya da ya nemi a sakaya sunansa.
Wani Birgediya – Janar mai ritaya wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ya kamata sojoji su sake tunani kan dabarunsu, ta hanyar lura da yadda maharan suke gudanar da ayyukansu ta yadda za su dakile abin da suke yi su samu nasara a kansu.
“Maharan sun amfani da wasu hanyoyi da ba saban ba a yakin da suke yi da sojojin. Suna amfani da bindigogin harbor jiragen sama da rokoki da gurneti wajen kai hare-hare ta kasa. Sojoji ba su yin haka a duniya, ” inji shi.
Ya ce, “Wannan dabara mayakan sunkuru ne ne ke yin ta saboda an takura musu, kuma za su yi ta jan yakin na shekaru. A irin haka sojoji kamata ya yi su bullo da wasu dabaru. Sun san abin da ya kamata su yi; kamata ya yi su kawo manyan bindigogi – kamar tankokin atilare da igwa-igwa, su gayyato sojojin sama. Kuma da sauran dabaru na zamani.”