Boko Haram na iya shafe Najeriya idan ba a tashi tsaye ba — Zulum

Zulum ya koka kan yadda mutane a jihar ke shiga Boko Haram da ISWAP.

Boko Haram na iya shafe Najeriya idan ba a tashi tsaye ba — Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi gargadin cewa rikicin Boko Haram na iya shafe kasar nan idan ba a tashi tsaye don shawo kan shi ba.

Ya yi gargadin ne lokacin da yake jawabi bayan ya karbi bakuncin kwamitin gudanarwa na Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) a zauren majalisar dokokin jihar da ke Maiduguri a ranar Litinin.

Ya ce, “Matsayin Jihar Borno a taswirar Najeriya yana da matukar muhimmanci a gare mu baki daya. Jihar Borno tana da iyaka da Chadi, Kamaru, da Jamhuriyar Nijar. Iyakokinmu sun yi yawa don haka tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas ya shafi tabbatar da tsaron kasa baki daya.

“Yayin da Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya da sauran su ke magana kan ’yan fashi, garkuwa da mutane, da sauran su, mu ’yan Boko Haram da ISWAP ne suka addabe mu. Yana da kyau a yi wani abu kafin su mallake jihar.

“Dole ne mu dakatar da daukar matasa daga shiga Boko Haram da ISWAP, idan ba haka ba, nan gaba kadan, za a shafe duk Najeriya daga taswira,” in ji Gwamna Zulum.

Yayin da yake kokawa kan yawan mutanen da ke gudun hijira, Gwamnan ya ce lamarin na kara ta’azzara sakamakon halin matsi da jama’a ke ciki.

“Sannan kuma a Jihar Borno, a 2012, kimanin mutane miliyan 3.5 ne suka rasa matsugunansu. Mun mayar da da yawa amma duk da haka, muna da sama da mutane miliyan daya: mutanen da suka rasa matsugunansu da ke zaune a sansanoni. Wasu na karuwanci, ana shaye-shayen miyagun kwayoyi a sansanonin,” a cewar Zulum.

“Saboda haka muna son hukumar ci gaban Arewa maso Gabas ta shiga tsakani. Muna son ku hada kai da gwamnatin jiha domin mu rufe wadannan sansanonin ‘yan gudun hijira domin mutane su samu abin dogaro da kansu.

“Idan ba haka ba, da yawa daga cikin mutanen za su iya shiga ISWAP da Boko Haram. Wadannan mutanen da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira abu ne mai matukar damuwa a gare mu duka. Don haka wannan aiki, na yi wa al’ummar Jihar Borno alkawarin cewa zan rufe duk wani sansani da ke cikin birnin Maiduguri kuma mun yi hakan da taimakon Allah Madaukakin Sarki.

“Yanzu burina na gaba shi ne ganin yadda za mu rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke sauran kananan hukumomin da babu zaman lafiya.”

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra