Boko Haram na shirin kai hare-hare kan fararen hula -Hukumar SS
Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta bukaci ’yan Najeriya su kara sanya ido tare da lura da tsaron kawunansu saboda hare-haren da sojoji ke kai wa Boko Haram a Arewa maso Gabas na iya harzuka ’ya’yan kungiyar su rika kai hare-hare ga fararen hula. A wata sanarwa da kakakin hukumar Marilyn Ogar, ta ce Hukumar SS […]
Hukumar Tsaron kasa (DSS) ta bukaci ’yan Najeriya su kara sanya ido tare da lura da tsaron kawunansu saboda hare-haren da sojoji ke kai wa Boko Haram a Arewa maso Gabas na iya harzuka ’ya’yan kungiyar su rika kai hare-hare ga fararen hula.
A wata sanarwa da kakakin hukumar Marilyn Ogar, ta ce Hukumar SS sakamakon yadda ake kai wa ’yan Boko Haram hare-hare tuni sun fara kai hare-hare ga wadanda ba su san hawa ba balle sauka.
Ta ce hare-haren da Boko Haram suka kai a baya-bayan nan a jihohin Yobe da Kano da Borno da Filato ana kaiwa ne domin raba hankalin hukumomin tsaro.
Hukumar ta ce ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa da sojoji ke yi kan mayakan Boko Haram a Arewa maso Gabas yana matukar raunana karfin ’yan ta’addan.
Marilyn Ogar, ta ce wannan ne ya sanya ’yan ta’addan suka koma huce fushinsu kan fararen hula da wuraren da suke da sauki kai musu hari.
Don haka ta bukaci masu kula da tashoshin mota su rika bincike kwakwaf kan motoci da fasinjoji da kayayyakin fasinjojin da suke shiga tasoshin.
Hukumar ta kuma bukaci masu kula da tasoshin motar su rika lura da sababbin ido da suke zuwa tashoshin a matsayin direbobi ko yaran mota. Kuma ta gargadi jama’a su rika lura tare da kauce wa shiga motocin da ba na daukar fasinja ba ne a kan hanyoyi.
Hukumar ta kuma bukaci mutanen garuruwan da aka sake kwatowa su koma garuruwansu.
Kuma ta ce, babu bukatar mutane su rika hijira zuwa wasu sassa na kasar nan, saboda zaben da ke tafe, “saboda hukumomin tsaro sun dauki matakan kare lafiya da dukiyar jama’a,” inji ta.
Hukumar ta kuma yi kira ga jama’ar da suke da bayanan da za su taimaka wajen fallasa ayyukan da ba su yarda da sub a, su hanzarta sanar da hukumomin tsaro.
“Muna son sake nanata yunukurin hukumomin tsaro na kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda da miyagu a kasarmu,” inji Hukumar SS din.