Boko Haram: Najeriya ba ta ba da hadin kai – Deby

Shugaban kasar Chadi Mista Idriss Deby, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta bayar da hadin kai a yunkurin da ake yi na murkushe kungiyar Boko Haram. Shugaban Chadin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata, inda suka […]

Boko Haram: Najeriya ba ta ba da hadin kai – Deby
Boko Haram: Najeriya ba ta ba da hadin kai – Deby

Shugaban kasar Chadi Mista Idriss Deby, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta bayar da hadin kai a yunkurin da ake yi na murkushe kungiyar Boko Haram.

Shugaban Chadin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata, inda suka tattauna cikin sirri.
Mista Deby ya shaida wa manema labarai a fadar da ke Abuja cewa “Abin takaici ne yadda sojojin Najeriya da na Chadi ba sa aiki cikin hadin gwiwa, kuma shi ne abin da ke kawo tsaiko a yaki da Boko Haram.”
Shugaba Deby kuma ya ce ba a kawar da Boko Haram baki daya ba, amma dai an yi musu illa sosai.
Ya ce da sojojin kasashen biyu suna aiki tare da yanzu an shafe Boko Haram daga bayan kasa.
Yaki da Boko Haram ya jawo makwabtan Najeriya ne saboda barazanar da kungiyar ke yi ga tsaron kasashen.
Sojoji kasar Chadi sun shigo Najeriya ne a farkon bana inda suka fafata da mayakan Boko Haram a garuruwan Damasak da Baga. Wannan ya taimaka wa sojojin Najeriya wajen kaddamar da hare-hare ga Boko Haram tun cikin watan Fabrairu, tare da kwato galibin garuruwan da suke hannunsu.
Shugaban na Chad wanda yake yawan sukar yadda Najeriya ke fuskantar yaki da Boko Haram din ya kuma gana da zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda suka tattauna a kan yadda Najeriya da Chadi za su ci gaba da hada kai wajen yakar kungiyar Boko Haram din.
Sojojin Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyyar Nijar na yaki da kungiyar Boko Haram a halin yanzu bayan da kungiyar ta fara gudanar da ayyukanta na ta’addanci a kasashen.