Boko Haram: Sarakuna bakwai sun gudu daga fadojinsu ** Mahara sun karbe fadoji da motocin sarakunan
Hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram ya tilasta sarakuna biyar daga cikin manyan sarakunan Jihar Borno takwas guduwa daga fadojinsu kamar yadda binciken Aminiya ya gano.Wasu sarakunan biyu a Jihar Yobe su ma an raba su da fadojinsu, bayan da mayakan suka karbe iko da masarautunsu.Sarakunan da lamarin ya shafa sun hada da Shehun Dikwa Alhaji […]
Hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram ya tilasta sarakuna biyar daga cikin manyan sarakunan Jihar Borno takwas guduwa daga fadojinsu kamar yadda binciken Aminiya ya gano.
Wasu sarakunan biyu a Jihar Yobe su ma an raba su da fadojinsu, bayan da mayakan suka karbe iko da masarautunsu.
Sarakunan da lamarin ya shafa sun hada da Shehun Dikwa Alhaji Muhammad Ibn Shehu Masta da Sarkin Gwoza Alhaji Muhammadu Ibn Mustapha Idrissa Timta, wadanda ’yan Boko Haram suka kame masarautunsu, sai Sarkin Bama Alhaji Kyari Ibn Ibrahim El-Kanemi, wanda ya gudu daga garinsa a ranar Litinin da ta gabata.
Sauran manyan sarakunan da aka raba da masarautunsu a Jihar Borno sun hada da Sarkin Askira Alhaji Abubakar Ibn Muhammad Askirama da takwaransa Alhaji Ali Ibn Isma’ila Mamza, Sarkin Uba, wadanda suka fice daga fadojinsu sakamakon rahotannin tsaro da ke cewa za a iya kai wa garuruwansu hare-hare.
kauyuka da dama da ke makwabtaka da su, an kai musu hari a bayan nan, kuma garuruwa Uba da Askira ba su da nisa daga garin Gwoza, wanda ’yan Boko Haram suka kwace a ranar 6 ga Agusta, kuma daga baya shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya ayyana ta a matsayin bangare na ‘Daular Musulunci.’
Garin Dikwa ma yana karkashin maharani tun ranar 28 ga Agusta, lamarin da ya tilasta dubban mutane gudu zuwa garin Maiduguri fadar jihar.
Kwana uku kafin nan mayakan Boko Haram sun kwace Gamboru wani gari da ke bakin iyaka da kasar Kamaru, wanda shi ma yake masarautar Dikwa bayan tafka fada da sojojin Najeriya.
Sarakuna uku da suke zaune a masarautunsu a Jihar Borno, wato Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi da Sarkin Shani Alhaji Nasiru Muhammadu Mailafiya da kuma Sarkin Biu.
‘Hawa motocin fada’
Mayakan Boko Haram a ’yan makonnin nan suna kara dannawa tare da kame sassa da daman a jihohin Borno da Yobe. Kuma akwai tsoron suna kara matsawa zuwa garin Maiduguri, inda dubban jama’a suka koma bayan kame garuruwansu.
“Muna karkashin mamaya. Sarakunanmu wadanda su ne masu kiyaye al’adunmu yanzu ba su tsira ba, mutanenmu suna mutuwa kowace rana kuma ga alama bala’in ci gaba yake yi,” inji wani lauya Barista Yusuf Modu Kabir.
Ya kara da cewa, “A yanayin da za a tilasta sarakunamu gudu daga masarautunsu, talakawansu suna gudun ceton rai, ba abu ne mai alheri ga kasar nan da take kiran kanta giwar Afirka ba.”
A shekara biyar da suka gabata, sarakuna da dama sun dandana kudarsu sakamakon nuna kyamarsu kan ayyukan ’yan Boko Haram.
A ranar 30 ga Mayun bana, mayakan Boko Haram sun bude wa sarakuna uku wuta a kanhanyarsu ta zuwa Gpmbe, inda a lokacin suka kashe Sarkin gwoza Alhaji Mustapha Idrissa Timta.
An kashe masu unguwanni (Lawanai) da dagatai (Bulama) da Hakimai da dama, yayin da wasu suka guje daga masarautunsu saboda tsoron Boko Haram.
A tattaunawa da manema labarai a kwanakin baya, Shehun Borno ya ce rikicin Boko Haram ya ci Hakimai 13 a masarautarsa
Sannan wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, sakamakon kwace garuruwa a Jihar Borno, kwamandojin Boko Haram ne suke hawa motocin Jeep-Jeep da Sarkin Gwoza ya gudu ya bari a matsayin ‘motocin aikinsu,’ inda suke zagayawa a cikin garin da kauyukan da suke kusa.
Wata majiya ta ce, “Akwai wani babban gidan mai a Gwoza da suke shan mai a motocinsu, sannan sun tilasta wani babban mai gidan burodi ya ci gaba da zama a Gwoza domin ya rika yi musu burodi.”
Majiyar ta ce, maharani sukab bayar da uamarni ga wadanda suke zaune a Gwoza da sauran garuruwan da suka kwace.
A Jihar Yobe maharani suna amfani da motocin da Sarkin Gujba da Sarkin Bara da ke karamar Hukumar Gulani suka gudu suka bari. An tabbatar da sarakunan biyu sun guje daga fadojibsu a daidai lokacin da ’yan Boko Haram ke dannawa yankunansu.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya ce, ’yann Boko Haram sun kwace garin Bara ne cikin ruwan sanyi ba tare da bude wuta ba, saboda an dauki lokaci babu wani jami’in tsaron a garin.
Wani mazaunin garin Bara da ya sulale zuwa garin Damaturu da ya
nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, ’yan bindigar sun sauka ne a masaukin baki na gwamnati mallakar karamar hukumar, kuma su ke iko da
garin Bara da sauran garuruwa da ke kusa kamar Gabai da Zango da Kukuwa da sauransu.