Boko Haram shirin Yahudawa ne da rubabbun Musulmi – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce lamarin Boko Haram shiri ne na Yahudawa da wasu rubabbun Musulmi.Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin rufe musabakar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 17 na kungiyar da aka gudanar a Kaduna.Ya […]

Boko Haram shirin Yahudawa ne da rubabbun Musulmi – Sheikh Jingir

Sheikh Muhammad Sani Yahaya JingirShugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce lamarin Boko Haram shiri ne na Yahudawa da wasu rubabbun Musulmi.
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin rufe musabakar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 17 na kungiyar da aka gudanar a Kaduna.
Ya ce, Allah Ya taimaka an kawo karshen matsalar Boko Haram sakamakon karya lagonta, yanzu kuma ’yan kungiyar asiri sun fara addabar Arewa ta wurin sace kananan yara, don haka ya yi kira ga matasa su fito da shirin gadin gari don kawar da wannan matsala.
Sheikh Jingir ya kuma ce kungiyar Izala ba ta tsibbu ba ce, domin haka duk malamin da ya je wurin wani mutum a kasar nan ya ce ya ba shi kudi don a yi masa addu’a a masallatan Izala to karya ya yi, domin kungiyar ba ta Allah Ya ba ku mu samu ba ce, kuma tana fada da bokaye da malaman da ke kokarin kawo wa addinin Musulunci cikas ne a kasar nan.
Sheikh Jingir ya kara da cewa wasu ne ke kokarin shafa wa kungiyar kashin kaji inda suke yada abubuwan da ba ta san da su ba, kamar cewa tana da marayu dubu 700 da sauran abubuwan da ba su dace ba, inda ya yi kira su ji tsoron Allah su daina su zo a ciyar da addini gaba.
Da ya juya kan shawarwarin da Dokta Ahmad Gumi ya ba kungiyar ya ce “Za mu yi aiki da shawarwarinka kuma za mu duba yiwuwar hana duk wanda bai kai shekara 20 hawa mumbarin Izala ya jagoranci kowane kwamiti na kungiya ba, kuma za mu rika daukar nauyin karatun wadanda suka zo na daya a gasar musabakar ta kungiya.”
Shugaban kwamitin raba kyaututtuka na musabakar Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya ce ’yan takara 136 ne suka fafata a mataki shida na gasar kuma sun kashe fiye da Naira miliyan 41, kan shirya gasar inda suka samu gudunmawar fiye da Naira miliyan biyar daga wurare daban-daban.
Malam Alhasan Yunusa daga Jihar Filato ne ya zama Gwarzon Shekara, inda Mai maraba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril Maigwari ya yi masa nadi a madadin Mai alfarma Sarkin Musulmi.
An raba motoci bakwai da babura da kekunan dinki da akwatunan talabijin da kujerun Hajji da kudi.
Sheikh Yusuf Sambo ya ba da sanarwa daukar nauyin karatun mutum biyar zuwa Uganda da wani bawan Allah ya yi.